NEC: Ana Rade Radin Kwace Kujerar Ganduje, APC Ta Tsaida Ranar Taron da Ake Jira
- Ana cikin jita-jitar sauyawa Abdullahi Ganduje mukami, jam'iyyar APC ta sanar da shirya babban taronta na Majalisar zartarwa
- Jam'iyyar APC ta sanya 12 ga watan Satumbar 2024 a matsayin ranar gudanar da taron NEC a birnin Tarayya, Abuja
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin sakataren jam'iyyar, Fetus Fuanter ya fitar a yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkita sanya ranar gudanar da babbar taronta na Majalisar zartarwa (NEC).
Jam'iyyar ta sanya ranar 12 ga watan Satumba 2024 domin gudanar da ganawar a birnin Tarayya, Abuja.
NEC: An sanya ranar taron jam'iyyar APC
Daily Trust ta ce ganawar NEC ita ce ta biyu mafi girma daga cikin tarurruka da ake daukar wasu muhimman matakai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin sakataren jam'iyyar, Barista Fetus Fuanter shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 15 ga watan Agustan 2024.
Fuanter ya ce masu ruwa da tsakin jam'iyyar za su gana a ranar 11 ga watan Satumba kafin gudanar da taron a washe-gari.
Ya ce a taron nasu sun goyi bayan kasancewar Cif Tony Okocha shugaban riko na jam'iyyar a jihar Rivers inda ya cancanci hukuncin kotu da ta kare shi.
Ganduje na iya rasa kujerar shugaban APC
Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar Shugaba Bola Tinubu zai sauyawa Abdullahi Ganduje muƙami.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu zai mayar da Ganduje muƙamin jakada a daya daga cikin ƙasashen Nahiyar Afirka.
Wata majiya ta ce hakan bai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi kan Ganduje a jihar Kano.
Zanga-zanga: Ganduje ya jefi Abba da zargi
Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan zanga-zanga da aka yi a jihar Kano.
Ganduje ya ce ya samu bayanan sirri masu muhimmanci da ke tabbatar da Abba Kabir ne ya dauki nauyin zanga-zangar.
Hakan ya biyo bayan zargin da Gwamna Abba Kabir ya yi cewa wasu matasa da aka ɗauki hayarsu sun da e takardun shari'ar Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng