Ana Zargin Batar Takardun Shari'a, Ganduje Ya Fadi Wanda Ya Dauki Nauyin Zanga Zanga

Ana Zargin Batar Takardun Shari'a, Ganduje Ya Fadi Wanda Ya Dauki Nauyin Zanga Zanga

  • A karshe, shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya bayyana wanda ya dauki nauyin zanga-zanga a jihar Kano
  • Ganduje ya ce akwai bayanan sirri da suka tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya dauki nauyin zanga-zangar
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce an yi hakan ne domin batawa gwamnatin Bola Tinubu suna tare da kawo mata tsaiko

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan zanga-zanga a Kano.

Ganduje ya ce ya samu bayanan sirri da ke tabbatar da Gwamna Abba Kabir ne ya dauki nauyin zanga-zangar.

Ganduje ya tona asirin wanda ya dauki nauyin zanga-zanga
Abdullahi Ganduje ya zargi Abba Kabir da daukar nauyin zanga-zanga. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje, @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Ganduje ya zargi Abba Kabir

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Edwin Olofu ya fitar a yau Alhamis 15 ga watan Agustan 2024, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ce an dauki nauyin zanga-zangar domin kara batawa gwamnatin Bola Tinubu suna da jawo mata matsala.

Tsohon gwamnan ya bukaci al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu yayin da aka ƙaddamar da bincike.

Har ila yau, Ganduje ya ce APC ta himmatu wurin tabbatar da kawo zaman lafiya a tsakanin al'umma da kwanciyar hankali.

Abba ya ce an sace takardun kotu

Wannan martani na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamna Abba Kabir ya zargi masu zanga-zanga da fakewa da ita wurin sace takardun shari'ar Ganduje da ake yi a kotu.

Gwamnan ya ce da gan-gan aka ɗauki hayarsu domin cimma manufar sace takardun da ake zargin Ganduje da cin hanci a jihar

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Ana hasashen Tinubu zai sauyawa Ganduje muƙami

Kun ji cewa akwai rahotanni da ke yawo da suka nuna cewa Bola Tinubu zai sauyawa Abdullahi Ganduje mukamin shugaban APC.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi kan tsohon gwamnan.

Ana hasashen Tinubu zai ba Ganduje muƙamin jakada a wasu daga cikin ƙasashen Nahiyar Afirka ko Asia ko kuwa Turai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.