Kungiyar Yarabawa ta Fara Shirin Tazarcen Tinubu, ta Tura Gargadi ga Yan Arewa
- Wata kungiyar Yarabawa ta yi magana kan masu neman sojoji su karbe mulkin Najeriya daga hannun Bola Ahmed Tinubu
- Shugaban kungiyar, Hammed Olalekan ya ce mulkin Najeriya na kowa da kowa ne kuma ya fadi yadda suke fata zaben 2027 ya kasance
- Haka zalika Hammed Olalekan ya yi kira ga matasan Arewa kan yadda ya kamata su fuskanci harkar siyasa a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Kungiyar Yarabawa ta YYSA ta yi kira na musamman ga yan Arewa kan zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Kungiyar ta ce maganar da ake ta cewa sojojin Najeriya su karbi mulkin Najeriya daga hannun Bola Tinubu ta saba dokar kasa.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta ce tana fatan Bola Tinubu zai lashe zabe a shekarar 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
YYSA: 'Yan Arewa su jira 2031'
Kungiyar Yarabawa ta YYSA ta ce dukkan yan Arewa da suke kiran cewa sojoji su karbi mulki daga hannun Bola Tinubu sai su jira shekarar 2027.
YYSA ta ce hakan na nuni da cewa shugaba Bola Tinubu zai zarce bayan an yi babban zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Magana kan zanga zanga a Arewa
Shugaban YYSA, Hammed Olalekan ya ce wasu yan siyasa ne suka dauki nauyin zanga zangar tsadar rayuwa a Arewa domin kawo cikas ga Tinubu.
Hammed Olalekan ya kara da cewa waɗanda suka gaza cin zabe da marasa kishin kasa ne ke son tayar da fitina da sunan zanga zanga.
YYSA ta yi kira ga matasan Arewa
Kungiyar YYSA ta yi kira ga matasa kan kaucewa rudin yan siyasa da suke sanya su fitowa kan tituna ba tare da dalili ba.
Kungiyar ta ce yan siyasar kawai suna son yin amfani da su ne domin cimma burinsu sannan su yi watsi da su.
APC ta shiga rikici a Benue
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin shugabancin jam'iyya ya kara ƙamari a jihar Benue yayin da ɓangare daya ya nufi yin taron masu ruwa da tsaki.
Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya gargadi ɓangaren da suke shirin shirya taron kan kaucewa tayar da fitina a jihar saboda siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng