Cin Hanci: Ganduje Ka Iya Rasa Kujerarsa, Watakila Tinubu Ya Sauya Masa Mukami
- Yayin da ake zargin shugaban APC, Abdullahi Ganduje da cin hanci, rahotanni sun bayyana cewa zai iya rasa kujerarsa
- Wata majiya ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu yana shirin sauyawa Ganduje mukami da na jakada a kasashen Afirka
- Hakan bai rasa nasaba da zarge-zargen da ake yi kan tsohon gwamna, Ganduje na cin hanci da rashawa a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ana hasashen Shugaba Bola Tinubu zai iya sauyawa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje mukami.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban zai iya mayar da Ganduje a matsayin jakada a kowace kasa da ke Nahiyar Afirka.
Tinubu na shirin raba Ganduje da kujerarsa
A wani rahoton na musamman da Daily Nigerian ta tabbatar, ta ce tuni aka sanar da Ganduje kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya da ta bukaci boye sunanta ta ce farko an tura shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio domin ya sanar da shi.
Majiyar ta ce Akpabio ya fada masa cewa Tinubu zai sauya masa muƙamin ne saboda shari'ar cin hanci da ake yi a Kano.
Ganduje ya ki amincewa da tayin Tinubu
Sai dai an ce Ganduje ya yi ki amincewa da tayin inda ya ce duk zargi ne babu wasu hujjoji kan haka.
"Ta wannan hanya Tinubu zai saka mania irin biyayya da na yi, na tsufa da karbar muƙamin jakada, duk zarge-zargen karya ne, zan yi nasara a kotu."
- Abdullahi Ganduje
Sai dai wata majiya ta ce Tinubu ya ba Ganduje zabin Nahiyoyin Afirka da Asia da kuma Turai.
An ce hankalin Ganduje ya tashi inda ya yi ta bin kafa har wurin Bisi Akande domin ganin ya cigaba da rike mukaminsa.
Sai dai da aka tuntubi kakakin Ganduje, Edwin Olofu ya ce mai gidansa bai fada masa komai game da sabon muƙamin ba.
Abba: An sace takardun shari'ar Ganduje
Kun ji cewa Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shari'ar zargin rashawa da ake yi wa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa an sace takardun da ake tattara bayanan shari'ar Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng