Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Yan Arewa Za Su Yi wa Tinubu a Zaben 2027

Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Yan Arewa Za Su Yi wa Tinubu a Zaben 2027

  • Fitaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya bayyana irin wahalar da Bola Tinubu zai sha a hannun mutanen Arewa a 2027
  • Fasto Ayodele ya ce shugaban zai fuskanci taron dangi daga 'yan Arewa wanda zai kawo masa cikas wajen neman tazarce
  • Ayodole ya yi magana kan yunkurin juyin mulki inda ya ce Ubangiji ba ya son hakan kuma ba zai bari hakan ya faru ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027, malamin addini ya yi hasashe mai rikitarwa.

Fasto Elijah Ayodele ya ce yan Arewa za su jazawa Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 wurin yin taron dangi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi babban darasin da gwamnonin Arewa suka dauka daga zanga zangar yunwa

Fasto ya fadi matsalar da Tinubu zai samu da yan Arewa
Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen Tinubu zai sha kaye a zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Elijah Ayodele.
Asali: Twitter

2027: Fasto ya yi hasashe kan Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Osho Oluwatosin ya fitar, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya ce hakan zai yi matukar yi wa Bola Tinubu wahalar samun nasarar lashe zaben a karo na biyu.

Ya ce yan Arewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun kifar da Tinubu a zaben da ake tunkara.

"Yan Arewa za su yi taron dangi ga Tinubu a zaben 2027 wanda zai yi masa wahalar samun nasara, za su yi duk mai yiwuwa domin kifar da gwamnatinsa."
"Duk da haka, babu wani juyin mulki da zai faru a Najeriya, duk mai shirya wannan ba zai samu nasara ba, Ubangiji ba ya son juyin mulki."

- Elijah Ayodele

Halin kunci: Fasto Ayodele ya shawarci Tinubu

Kara karanta wannan

Ribar zanga zanga: An fara maganar yunkurin inganta rayuwa a Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Malamin addinin ya bayyana cewa manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin APC sun yi tsauri kuma sun ƙara rura wutar wahalar da ake sha a ƙasa.

Primate Ayodele ya bayyana cewa da gwamnati mai ci na ɗaukar shawara da ta yi wa saura zarra, amma manufofin da ta zo da su ba su amfani ƴan ƙasar nan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.