Tsohon Kwamishina ya Gaskata Dan Bello kan Zargin Matar Ganduje da Wawushe N20bn

Tsohon Kwamishina ya Gaskata Dan Bello kan Zargin Matar Ganduje da Wawushe N20bn

  • Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, ya yi magana kan bidiyon da Dan Bello ya sake a kan matar Abdullahi Ganduje
  • Mu'azu Magaji ya yi magana da ke nuni da cewa zargin da Dan Bello ya yi ga matar tsohon gwamnan Kano zai iya zama gaskiya
  • Legit ta tattauna da wani matashi, Manga Adamu Hamza kan jin ra'ayinsa a kan tone tone da Dan Bello ya fara a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Kallo ya koma sama tsakanin mai bidiyon barkwanci, Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Dan Bello da jam'iyyar APC a jihar Kano.

Dan Bello ya wallafa wani bidiyo da ya zargi matar shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da wawushe kudin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ana zargin batar takardun shari'a, Ganduje ya fadi wanda ya dauki nauyin zanga zanga

Dan Bello
Mu'azu Magaji ya yi martani kan bidiyon Dan Bello. Hoto: Muaz Magaji|Dan Bello
Asali: Facebook

Tsohon kwamishinan ayyukan Kano a mulkin Ganduje, Mu'azu Magaji ya yi tsokaci kan lamarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin Dan Bello kan matar Ganduje

Mai wasan barkwanci a kafafen sada zumunta, Dan Bello ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook yana zargin matar shugaban APC na kasa da wawushe akalla N20bn a jihar Kano.

Dan Bello ya zargi Hafsat Abdullahi Ganduje da awon gaba kudin ne daga asusun gwamnatin Kano inda ya ce ta bude asusun banki 44.

Bidiyon da Dan Bello ya fitar a kan matar Ganduje na cigaba da jan hankulan al'umma musamman a jihohin Arewacin Najeriya

N20bn: Martanin kwamishinan Ganduje

Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano, Mu'azu Magaji ya ce abin da Dan Bello ya fada kadan ne cikin abin da za ta iya aikatawa.

Mu'azu magani ya ce halin bera na cikin abin da ya faru a mulkin Abdullahi Umar Ganduje a kusan dukkan ma'aikatun gwamnati.

Kara karanta wannan

Cin hanci: Ganduje ka iya rasa kujerarsa, watakila Tinubu ya sauya masa mukami

Tsohon kwamishinan ya kara da cewa irin halin ne ya sanya shi fada da gwamnatin Abdullahi Ganduje tun a karon farko.

Muaza Magaji

Legit ta tattauna da Manga Adamu

Manga Adamu Hamza ya zantawa Legit cewa abubuwan da Dan Bello yake za su taimaka wajen wayar da kan al'umma.

Sai dai yace bayyana wasu abubuwa da suka shafi rayuwar mutane kamar lambar BVN bai kamata ba a ra'ayinsa.

Dan Bello ya caccaki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fito ya ƙara yi wa shugaba Bola Tinubu wankin babban bargo.

Dan Bello ya bayyana cewa ƴan Najeriya na fama da yunwa saboda tsare-tsaren da gwamnati mai ci ta Bola Ahmed Tinubu ta kawo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng