'Yan Majalisa Sun Fusata da Kalaman Obasanjo, Sun Karyata Zargin Kayyade Albashinsu

'Yan Majalisa Sun Fusata da Kalaman Obasanjo, Sun Karyata Zargin Kayyade Albashinsu

  • Majalisar dattawa ta yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo martani kan zargin cewa ita ke tantance albashin ‘ya 'yanta
  • Haka zalika, tsohon shugaban ya zargi 'yan majalisar da karbar wasu kudi na musamman daga kasafin kudi a hannun Bola Tinubu
  • Yemi Adaramodu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, ya bayyana maganar Obasanjo a matsayin 'karya'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar Dattawa ta yi kakkausar suka kan zargin da ake yi mata na cewa ita ce ke kayyade albashinta da kuma karbar wasu kudaden tukuici na kasafin kudi daga shugaban kasa.

An ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya yi ikirarin a ziyarar da ‘yan majalisar tarayya suka kai masa, zargin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya aike da saƙon gaggawa ga Tinubu kan masu zanga zanga

Majalisar dattawa ta mayarwa Obasanjo martani kan ikirarin kayyade albashin 'yan majalisa
Majalisar dattawa ta 10 ta yiwa Obasanjo martani kan zargin kayyade albashi. Hoto: Nigerian Senate, Olusegun Obasanjo
Asali: Facebook

Majalisar tarayya ta karyata zargin Obasanjo

Majalisar ta yi martanin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar dattawa, Yemi Adaramodu (APC, Ekiti ta Kudu) ya saki a ranar Lahadi, inji rahoton Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ruwaito majalisar ta bayyana zargin tsohon shugaban kasar a matsayin wani yunkuri na "cin dunduniyar majalisar ta hanyar jifarta da wadannan karairayi.”

Adaramodu ya jaddada cewa babu wani sanata da ya samu tallafin kudi daga fadar shugaban kasa da sunan 'tukuici' na kasafin kudi.

Majalisar tarayya ta kalubalanci Obasanjo

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, sanarwar ta fayyace cewa ayyukan mazabu da ake dangantawa da majalisa, sanatoci ne kawai ke ba da shawarwari da kuma tantance su.

Da yake kara bayani, Adaramodu ya ce majalisar dattawa tana karbar albashin da hukumar tattara kudaden shiga ta kasafta mata ne kawai kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

NNPC ke yiwa tattalin arziki zagon kasa? Kyari ya wanke kamfanin Najeriya

Majalisar dattawan, ta kalubalanci Olusegun Obasanjo da ya bayar da hujjojin da ke nuna cewa 'yan majalisar ne suka kayyade albashin da ake biyansu a halin yanzu.

Abin da Obasanjo ya fadawa 'yan majalisa

Tun da fari, mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya zargi majalisar dokokin kasar da kayyade albashin su da kansu.

Obasanjo ya kuma yi zargin cewa bangaren zartarwa na biyan ‘yan majalisar tarayya kudin da ba su cancanci samu ba kuma suna karba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.