Sanatan APC Ya Yafewa Wadanda Suka Tafka Masa Barna Lokacin Zanga Zanga
- Yayin da masu zanga-zanga suka yi barna a jihar Jigawa, Sanatan APC a jihar ya yafewa wadanda suka tafka masa barna
- Sanata Babangida Hussaini da ke wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ya ce abin takaici ne yadda aka yi barna a jihar
- Sanatan ya jajantawa al'ummar jihar musamman wadanda suka rasa dukokiyoyi da rayuka yayin zanga-zangar da aka yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jigar Jigawa - Sanata a jihar Jigawa ya bayyana cewa ya yafewa duk wadanda suka masa barna yayin zanga-zanga a jihar.
Sanata Babangida Hussaini da ke Wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ya ce duk da asasar da ya tafka na miliyoyi amma ya yafe.
Zanga-zanga: Sanata ya yafewa yan Jigawa
Yafiyar sanatan ya biyo bayan hari kan gonarsa da aka yi inda aka sace dabbobi da kayan gona na miliyoyi, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a mazabar Kazaure da ke jihar yayin gudanar da zanga-zanga da aka yi na kwanaki a fadin kasar.
Matasan sun yi yunkurin kona gidan sanatan da ke Kazaure kafin jami'an tsaro su yi nasarar dakile shirin nasa.
Jigawa: Sanata ya jajantawa jiharsa kan zanga-zanga
"Miyagu sun kai farmaki gonata da ke Gada duk da kokarin jami'an tsaro na dakile su inda suka lalata gonar tare da sace kayan da ke ciki."
"Daga cikin kayan akwai tagogi da kofofi da kuma dabbobi da tsuntsaye na makudan miliyoyin nairori."
"Bana fushi kan haka kuma babu abin da zai kawar min da hankali kan ayyukan cigaba ga 'yan mazabata ba."
- Sanata Babangida Hussaini
Sanatan ya jajantawa wadanda suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.
CAN ta bukaci addu'o'i saboda ruwan sama
Kun ji cewa Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Taraba ta ba da umarnin yin azumi da addu'o'i na tsawon kwanaki uku.
Kungiyar ta matasan CAN ta dauki wannan matakin ne domin neman taimakon Ubangiji saboda rashin ruwan sama da aka dade babu a jihar.
Asali: Legit.ng