Zaben 2027: Yaron El Rufai Ya Yi Martani Kan Batun Hadakar Mahaifinsa da Peter Obi
- Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Bashir El-Rufai, ya musanta raɗe-raɗin yin haɗaka tsakanin mahaifinsa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi
- Ya bayyana jita-jitar a matsayin ƙarya ce tsagwaronta a martanin da ya wallafa a shafinsa na X bayan wani ya yi iƙirarin cewa ƴan siyasan biyu za su yi haɗaka
- An yi ta raɗe-raɗin cewa akwai rashin jituwa tsakanin El-Rufai da Bola Tinubu bayan majalisar dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa domin zama minista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Bashir El-Rufai, ɗaya daga cikin ƴaƴan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan yiwuwar yin haɗaka tsakanin mahaifinsa da Peter Obi.
Bashir El-Rufai ya yi watsi da raɗe-raɗin da ke cewa mahaifinsa zai yi haɗaka da ɗan takarar na zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
El-Rufai ya samu saɓani da Tinubu
El-Rufai ya taka rawar gani a kan nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023, sannan an zaɓe shi domin samun kujerar minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, majalisar dattawa ta ƙi amincewa da naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa.
Tun a wancan lokaci ake ta raɗe-raɗin cewa alaƙar siyasa tsakanin tsohon gwamnan na Kaduna da Tinubu ta ruguje, kuma yana iya yin adawa da shugaban ƙasan idan ya nemi tazarce a zaɓen 2027.
Bashir El-Rufai ya yi martani kan haɗakar El-Rufai da Peter Obi
A na cikin wannan raɗe-raɗin, wani mai amfani da sunan Hon. Dan_Borno, @DanBornoReal, a shafin X, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan gwagwarmayar siyasa ya ce akwai yiwuwar haɗaka tsakin El-Rufai da Peter Obi.
"Akwai jita-jita na yiwuwar yin haɗaka tsakanin Peter Obi da Nasir Ahmed El-Rufai."
- Hon. Dan_Barno
Da yake mayar da martani a shafinsa na X Bashir El-Rufai ya musanta hakan.
"Ƙarya ce tsagwaronta daga kogin Ezu a Anambra."
- Bashir El-Rufai
Karanta wasu labaran kan El-Rufai
- El Rufai ya sake caccakar Uba Sani, ya fadi makarkashiyar da aka yi masa
- Kaduna: Tsofaffin kwamishinoni sun fadi gaskiya kan zargin El Rufai ya wawure N423bn
- Badakalar N423bn: Dan majalisa ya yiwa El-Rufai wankin babban bargo
Kwankwaso ya gayyaci El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan bude kofa da suka yi ga duk mai son shiga jam'iyyar NNPP.
Kwankwaso ya ce suna maraba da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai idan zai shigo jam'iyyar.
Asali: Legit.ng