Kwankwaso: Dan Majalisar NNPP Ya Gargadi Tinubu, APC lan Illar Alhassan Doguwa

Kwankwaso: Dan Majalisar NNPP Ya Gargadi Tinubu, APC lan Illar Alhassan Doguwa

  • Dan Majalisar Tarayya a Kano, Abdulmumin Jibrin ya bayyana Alhassan Doguwa a matsayin barazana ga zaman lafiyar jihar
  • Jibrin ya bayyana haka ne yayin da yake takun saka da takwaransa a Majalisar Wakilan daga Kano kan kalamansa
  • Wannan na zuwa ne bayan Jibrin ya gargadi Alhassan Doguwa kan caccakar Satata Rabiu Kwankwaso a kwanakin baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dan Majalisar Tarayya a jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya yi magana kan kalaman dan Majalisa, Alhassan Doguwa.

Jibrin ya ce Doguwa barazana ne ga jam'iyyar APC da kuma shi kansa shugaban kasa, Bola Tinubu.

Dan Majalisar NNPP ya caccaki Alhassan Doguwa kan kalamansa ga Kwankwaso
Abdulmumin Jibrin ya fadi illar Alhassan Ado Doguwa ga Tinubu da APC. Hoto: Abdulmumin Jibrin, Alhassan Ado Doguwa.
Asali: Facebook

Kwankwaso: Jibrin ya caccaki kalaman Alhassan Doguwa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar 10 ga watan Agustan 2024, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisa ya magantu kan farmaki yayin taro da Aminu Ado ya halarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jibrin ya ce kalaman Doguwa za su iya jawo babbar matsala musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Dan Majalisar da ke jam'iyyar NNPP da Alhassan Doguwa a APC a cikin 'yan kwanakin nan suna cigaba da caccakar junansu.

Jibrin ya fadi illar Doguwa ga Tinubu

"Duk wata zanga-zanga ko da ta lumana ce tana da illolinta ga kasa baki daya."
"Na yi imanin cewa mutane kamar su Doguwa barazana ne ga jam'iyyarsa da kuma Bola Tinubu saboda kalamansa da ke neman kawo cikas a Kano."
"Doguwa ya na ta kokarin sai ya saka wasu musamman shubannin jam'iyyarsa kan wannan korafin da na yi kansa game da sukar Sanata Rabiu Kwankwaso."

- Abdulmumin Jibrin

Jibin ya ce bai kamata Alhassan Doguwa ya ci mutuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an gindaya masa sharuda

Doguwa ya caccaki dan Majalisar NNPP

Kun ji cewa shugaban kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da albarkatun man fetur, Alhassan Doguwa ya mayar da martani ga Abdulmumin Jibrin.

Alhassan Ado Doguwa ya mayar da martanin ne bisa zargin cewa ya ci mutuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A wata sanarwa da ya fitar, Ado Doguwa ya bayyana cewa yana mutunta Kwankwaso duk da saɓanin da ke tsakaninsu a siyasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.