Gwamna Abba Kabir Ya Fadi Babbar Illar da Ganduje Ya Yi Wa Kano, Ya Dauki Mataki
- Gwanatin jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda aka samu cin hanci fiye da ko yaushe a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Ganduje ya kassara jihar musamman wurin cin hanci da rashawa wanda ya yi muni
- Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta bukaci gudanar da bincike kan rabon shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya bayyana damuwa kan salon mulkin tsohon gwamna, Abdullahi Ganduja.
Gwamnan ya ce Kano ta fuskanci mafi munin cin hanci da rashawa fiye da ko yaushe a lokacin mulkin Ganduje.
Abba ya caccaki Ganduje kan cin hanci
Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin taron karawa juna sani na ma'aikata a jihar kan cin hanci, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce Kano ta fi kowace jiha samun matsala game da cin hanci a mulkin Ganduje daga 2015 zuwa 2023.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo wanda ya wakilci gwamnan ya ce cin hanci ke dakile cigaba a kasa, Daily Post ta tattaro.
Illar da Ganduje ya yi wa Kano
"Jihar Kano ta fi kowace jiha shiga matsala musamman a yankin Arewa maso Yamma game da matsalar cin hanci da rashawa."
"Kadarorin jihar Kano da dama an siyar da su ba bisa ka'ida ba kuma manyan ayyukan jihar an watsar da su wanda na daga cikin matsaloli da muke fuskanta bayan karbar mulki."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Gwarzo ya ce cin hanci a lokacin mulkin Ganduje ya kassara bangaren samar da ruwan sha wanda ya jawo karancin ruwa.
Mataimakin gwamnan ya ce hakan ya faru duk da karbar bashin Yuro 6m a bangaren domin kawo sauya.
Kano: APC ta yi zargi kan rabon shinkafa
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta ba gwamnatin Kano da wasu jami’ai suka yi.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci da a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kwamitin bincike mai zaman kansa.
Asali: Legit.ng