"Gidan Yari Ya Dace da Su": Obasanjo Ya Koka Kan Halin Shugabanni
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fadi yadda yan siyasa da shugabanni ya kamata su kasance yayin jagoranci
- Obasanjo ya ce mafi yawansu ba su da tarbiyya ko halayya na kwarai saboda ba gyaran kasa ba ne a gabansu
- Ya ce mafi yawansu sun fi dacewa a kulle su a gidajen gyaran hali saboda salon yadda suke gudanar da mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana takaici yadda shugabanni ke gudanar da mulki a yanzu.
Obasanjo ya ce ya kamata mafi yawansu suna garkame a gidan yari ne madadin rike da manyan ofisoshin gwamnati.
Obasanjo ya Allah wadai da halin shugabanni
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun yayin ganawa da mambobin Majalisar Tarayya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya ce mafi yawan shugabanni a yanzu ba su da tarbiyya da kuma gaskiya da ya kamata su jagoranci Najeriya, Daily Trust ta tattaro.
Ya ce ya kamata a sake zama kan tsarin shugabanci da ake gudanarwa a yanzu musamman da ke karkashin jagorancin gurbatattun shugabanni.
Obasanjo ya fadi inda ya dace da shugabanni
"Ya kamata mu sake zama kan tsarin mulkin da ake bi, amma babu gaskiya da kuma amana ga wadanda ke mulkarmu, cikin girmamawa gaskiya ya kamata suna gidan yari ne ko a rataye su."
"Idan irin wadannan shugabannin ne ke mulkarmu ta yaya kake tsammanin a samu cigaba."
"Abin da aka fi buƙata shi ne halayyarsu da kuma gaskiya da rikon amana."
- Cif Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya tona asiri kan tallafi mai a Najeriya
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce ana cigaba da biyan kudin tallafin mai a boye duk da cirewa da aka yi.
Obasanjo ya koka kan yadda ake cikin matsin halin kunci da kuma tsadar rayuwa wanda ya tilasta fara zanga-zanga a fadin kasar.
Tsohon shugaban kasar ya ce matasa da suke zanga-zanga neman hakkinsu suke duba da halin matsin da aka jefa su ciki na tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng