Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Matsala kan Sukar Tinubu, an Gindaya Masa Sharuda

Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Matsala kan Sukar Tinubu, an Gindaya Masa Sharuda

  • Kwana daya bayan kalaman Gwamna Bala Mohammed ga Bola Tinubu, kungiya ta ragargaji gwamnan kan neman rigima
  • Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta gargadi gwamnan da ya janye kalamansa tare da neman afuwar Shugaba Tinubu
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan adawar ya caccaki tsare-tsaren Tinubu inda ya ce sune silar jefa al'umma cikin kunci a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta gargadi Gwamna Bala Mohammaed na jihar Bauchi kan kalamansa.

Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta yi gargadin ne bayan gwamnan ya yi shagube ga Bola Tinubu kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

An gargadi gwamnan PDP kan caccakar Tinubu
Matasan Arewa sun bukaci Gwamna Bala ya ba Bola Tinubu hakuri. Hoto: Senator Bala Mohammed, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu: Matasa sun caccaki Gwamna Bala Mohammed

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta kungiyar ta fitar da Legit ta samu a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta zargi gwamnan da daukar nauyin zanga-zanga domin bata gwamnatin Bola Tinubu saboda kawo rudani, cewar Daily Post.

Har ila yau, kungiyar ta ce kalaman gwamnan ya yi su ne da gan-gan domin kawar da hankulan mutane kan cigaba da Tinubu ya kawo.

Matasan sun bukaci Gwamna Bala ya nemi afuwa ga Shugaba Tinubu tare da janye kalamansa inda suka ce 'yan Najeriya ba za su amince ba.

Daga karshe sun bukaci gwamnan ya mayar da hankali wurin kawo ayyukan raya kasa ga al'ummar jiharsa madadin sukar Tinubu.

Kalaman Gwamna Bala da suka fusata matasa

Wannan martani na kungiyar matasan na zuwa ne bayan Bala Mohammed ya caccaki tsare-taren Tinubu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ya gama sukar Tinubu, matsala 1 ta taso Gwamnan PDP ya nemi agajin Shugaban kasa

Kaura ya ce duk wahalar da aka shiga a kasar sanadin manufofin Tinubu ne marasa kyau da suka jefa al'umma cikin yunwa.

Gwamnan ya yi shagube ga Tinubu inda ya ce zai ba shi daraktan kamfe na PDP a zaben 2027 idan bai sauya salo ba.

Zanga-zanga: An bukaci korar shugaban 'yan sanda

Kun ji cewa Kwamitin gudanar da zanga-zanga a Najeriya ya bukaci daukar mataki kan sifeta-janar na 'yan sandan kasar.

Kwamitin ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukamin shuigaban 'yan sandan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.