Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Aike da Sakon Gaggawa Ga Tinubu Kan Masu Zanga Zanga
- Cif Olusegun Obasanjo ya gargaɗi gwamnatin tarayya ta biya bukatun matasa masu zanga zanga saboda suna kan gaskiya
- Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ta samu koma baya bayan ya bar mulki saboda waɗanda suka biyo bayansa ba su yi abin da ya dace ba
- Obasanjo ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi bakuncin ƴan majalisar wakiali shida a gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce matasan da suka fita zanga-zanga kan tsadar rayuwa suna kan gaskiya kuma ya kamata a saurari kokensu.
Obasanjo ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar wakilai shida wadanda suka kai kudirin dokar wa’adi daya na shekara shida ga shugaban ƙasa.
Daily Trust ta ce ƴan majalisar sun buƙaci rika karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu, sannan kujerar gwamna ta rika kewaya wa tsakanin mazaɓun sanatoci uku a kowace jiha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan majalisar dai sun gana da Obasanjo ne ƙarƙashin jagorancin Hon. Ugochinyere Ikenga mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Ideato ta Kudu a jihar Imo.
A jawabinsa, Obasanjo ya ce gwamnatocin da suka shuɗe sun sauka daga kan tubalin da ya kafa a lokacin mulkinsa, yana mai cewa hakan ya jawo koma baya.
Zanga-zanga: Obasanjo ya ba Tinubu mafita
"Abubuwan da matasa masu zanga-zanga suka buƙata bai saɓa doka ba kuma ya kamata a saurare su da kunnen basira, taya ƙiri-ƙiri za a ƙwace masu abin da dama mallakinsu ne?
"Suna cikin takaici da ƙuncin rayuwa, suna jin yunwa, sun fusata, ba su da aikin yi, sun cancanci a zauna a saurare su," in ji Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta biyan buƙatun matasan da ke zanga-zanga a kasar nan domin su na kan gaskiya, in ji PM News.
Obasanjo ya ja kunnen shugabanni
A wani rahoton kuma tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi shugabanni a kasar nan kan matsalar da ke tunkaro wa
Dattijon kasar ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta cigaba ba matukar shugabanni da 'yan kasa ba za su rungumi hakuri ba.
Asali: Legit.ng