Zanga Zanga: Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Gana da Ƴan Majalisar Tarayya 6, Bayanai Sun fito
- Ƴan majalisar tarayya shida karƙashin jagorancin Hon. Ikenga Ugochinyere sun yi ganawar sirri da Olusegun Obasanjo a Abeokuta
- Bayanai sun nuna tsohon shugaban ƙasar ya tattauna muhimman batutuwa da suka shafi Najeriya a wannan taro na ranar Jumu'a
- Wannan dai na zuwa ne bayan abubuwa marasa daɗi da suka faru a sƙasar nan lokacin zanga zangar adawa da manufofin gwamnnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasango ya yi ganawar sirri da ƴan majalisar wakilai shida a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
Ƴan majalisar sun shiga wannan taro wanda ke gudana a gidan Obasanjo ƙarƙashin jagorancin Hon. Ikenga Ugochinyere, mai wakiltar mazaɓar Ideato ta Kudu da ta Arewa.
Me za a tattuna a taron?
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, ana sa ran ƴan majalisa za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa tare da tsohon shugaban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran ‘yan majalisar da suka halarci taron sun hada da Hon. Peter Aniekwe, Hon. Matthew Nwogu, Hon. Abdulmaleek Danga, Hon. Midala Usman, da Hon. Kama Nkemkanma.
Da yake jawabi bayan fitowa daga taron, Obasanjo ya jaddada cewa Najeriya ba za je ko ina ba ta fannin ci gaba har sai shugabanni da talakawa sun gyara halayensu.
Obasanjo ya gargaɗi shugabanni
Ya yi gargadin cewa Najeriya na kan ƙaya wanda ka iya rugujewa da ita idan al’umma suka gaza daukar kwararan matakan da suka dace wajen magance dimbin kalubalen da ake fama da su.
Kamar yadda Punch ta ruwaito, Obasanjo ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da ke tangal-tangal, tana kwan-gaba kwan-baya.
Bugu da ƙari, tsohon shugaban kasar ya ce buƙatun masu zanga-zanga suna kan hanya kuma ya kamata gwamnati ta zauna da su ta saurare su.
Gwamna ya maida martani ga Tinubu
A wani rahoton kuma Gwamna Seyi Makinde ya musanta ikirarin Bola Ahmed Tinubu na rabawa jihohi N570bn domin ragewa al'umma raɗaɗin kuncin rayuwa
Tun farko shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta rabawa gwamnoni maƙudan kuɗi domin su faɗaɗa shirye-shiryen tallafawa ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng