“Zan Gayyace Ka Zama Daraktan Kamfen PDP a 2027”: Gwamna Ya Yi Shugube ga Tinubu

“Zan Gayyace Ka Zama Daraktan Kamfen PDP a 2027”: Gwamna Ya Yi Shugube ga Tinubu

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya yi magan kan zaben 2027
  • Gwamna na Bauchi ya ce tsare-tsaren Bola Tinubu a Najeriya sun jefa al'umma cikin mawuyacin hali inda ya bukaci sauyi
  • Bala Mohammed ya ce idan bai gyara ba to tabbas zai sha mamaki a zaben 2027 domin ko ina zai zama PDP ake muradi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sake caccakar Bola Tinubu kan yadda ake gudanar da mulki.

Sanata Bala Mohammed ya ce zai gayyaci Bola Tinubu ya zama daraktan kamfe na jam'iyyar PDP a zaben 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

Gwamna PDP ya gargadi Tinubu kan tsare-tsarensa a Najeriya
Gwamna Bala Mohammed ya ce Bola Tinubu zai sha mamaki a zaben 2027. Hoto: Bala Mohammed, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

2027: Gwamnan Bala ya gargadi Tinubu

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kamfe na zaben kananan hukumomi a wani bidiyo da AIT ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Mohammed ya ce kwata-kwata tsare-tsaren Tinubu ba su aiki sai dai kawai sake jefa al'umma cikin mummunan yanayi.

Ya koka kan yadda rashin aikin yi ya yi kamari ga talauci da kuma rashin ingantaccen ilimi da za a ba al'umma.

Gwamnan ya kalubalanci Tinubu kan tsare-tsarensa

"Rashin aikin yi ya yawa, harkar ilimi ya lalace, duka tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya ba su aiki dole su fahimci haka."
"Wadannan matsaloli da muke fuskanta su ne silar wahalar da muke cikin yanzu dole ne su sauya tsare-tsarensu."
"Idan hakan ya cigaba da tafiya, zan gayyace shi ya zama daraktan kamfe na jam'iyyarmu saboda ko ina zai zama PDP ne."

- Bala Mohammed

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi darasin da ya kamata gwamnonin Arewa su dauka kan zanga zanga

Gwamna Bala ya ce PDP za ta yi nasara a zaben saboda tsananin wahalar da mutane suke ciki a yanzu a fadin kasar.

Halin kunci: Izalah ta bukaci fara Alkunut

Kun ji cewa Shugaban Izalah reshen Kaduna, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sake magana kan fara addu'o'i ga Najeriya da shugabanninta.

Sheikh Bala Lau ya ce addu'o'in da za a yi sun hada da neman shiriyar shugabanni da sojoji da 'yan sanda da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.