Zanga Zanga: A Karshe, Ganduje Ya Yi Magana, Ya Tura Sako ga ’Yan Najeriya

Zanga Zanga: A Karshe, Ganduje Ya Yi Magana, Ya Tura Sako ga ’Yan Najeriya

  • Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya yi magana kan halin kunci da 'yan kasar ke ciki wanda ya tilasta zanga-zanga
  • Abdullahi Ganduje ya ba da tabbacin cewa tsare-tsaren Bola Tinubu suna kan hanya kuma suna daf da ba da sakamako mai kyau
  • Wannan martani na Dr. Ganduje ya na zuwa ne yayin da 'yan kasar suke cikin zanga-zanga saboda tsadar rayuwa da ake ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan halin kunci da ake ciki.

Abdullahi Ganduje ya ce wannan hali da ake ciki na lokaci kadan ne komai zai wuce kamar ba a yi ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi masu adawa da matatar man Dangote, 'yan Najeriya sun yi martani

Ganduje ya roki 'yan Najeriya karin hakuri kan halin kunci da ake ciki
Yayin da ake cigaba da zanga-zanga, Abdullahi Ganduje ya roki 'yan Najeriya. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Ganduje ya roki 'yan Najeriya

Shugaban APC ya bayyana haka ne a Abuja yayin tarbar tawagar 'yan jam'iyyar daga Amurka a sakatariyarta a Abuja, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kano ya ce tsare-tsaren Bola Tinubu tabbas za su kawo sauyi nan ba da jimawa ba, cewar The Guardian.

Ganduje ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri inda ya ce daman idan za a yi gyara dole a samu matsaloli na wani lokaci.

Ganduje ya ce komai ya kusa wucewa

"Babu tantama ko a kasashen da suka cigaba sun fuskanci irin wannan matsala, ba abin mamaki ba ne Najeriya ta tsinci kanta a ciki."
"Wannan ba shi ne karon farko ba, idan za ku tuna kowane sauyi na cigaba dole ya zo da kalubale."
"Saboda haka dole mutane su sha wahala, amma a gaba kadan za a ci moriyar wahalar da ake sha a yanzu."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jigon APC ya nemowa Tinubu mafita kan masu daga tutar Rasha

- Abdullahi Ganduje

Martanin Ganduje na zuwa ne yayin da matasa suka fantsama tituna domin gudanar da zanga-zanga.

Kano: Ganduje ya tallafa da makudan kudi

Kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika tallafin N5.3m ga wadanda iftila'in harin masallaci ya rutsa da su.

Matashi Shafi'u Abubakar mai shekaru 38 ne ya watsawa masallata fetur kana ya cinna musu wuta suna tsaka da sallah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.