Zanga Zanga: Jigon APC Ya Nemowa Tinubu Mafita Kan Masu Daga Tutar Rasha

Zanga Zanga: Jigon APC Ya Nemowa Tinubu Mafita Kan Masu Daga Tutar Rasha

  • Yayin da ake cigaba da zanga-zanga, jigon APC ya shawarci Bola Tinubu kan abin da ya kamata ya yi game da daga tutucin Rasha
  • Jagoran jam'iyyar mai suna Podar Johnson Yiljwan ya ce dole Tinubu ya kira su domin bayyana dalilinsu na daga tutocin a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu daga cikin masu zanga-zanga suke daga tutar kasar Rasha wanda ya dauki hankalin jama'a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar APC ya yi magana kan masu daga tutocin kasar Rasha inda ya shawarci Bola Tinubu kan haka.

Podar Johnson Yiljwan daga jihar Plateau ya shawarci Tinubu ya kira shugabannin masu zanga-zanga kan alakar tutar kasar Rasha da korafinsu.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Manyan 'yan siyasa da kungiya da suka kushe jawabin Tinubu

Jigon APC ta shawarci Tinubu game da masu daga tutar Rasha a zanga-zanga
Jigon APC ya bayyana damuwa kan masu daga tutar Rasha inda ya ba Bola Tinubu shawara. Hoto: Podar Johnson, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tutocin Rasha: Jigon APC ya shawarci Tinubu

Yiljwan ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Legit inda ya ce ya kamata matasa sun janye zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na APC ya ce babu tsari kwata-kwata a zanga-zangar illa cigaba da takura al'umma da kuma kara tashin hankali a kasa.

Ya ce zanga-zangar barazana ce ga zaman lafiyar Najeriya inda ya ce wasu masu mugun nufi sun kwace ikonta a kasar.

'Dan APC ya bukaci janye zanga-zanga

"Tabbas ya kamata su janye wannan zanga-zanga da suke yi saboda ba su da tsari illa cigaba da wahalar da al'umma da lalata dukiyoyi."
"Ya kamata Bola Tinubu ya kira su domin su yi bayani kan dalilin daga tutucin Rasha a kasa mai 'yanci kamar Najeriya."
"Wannan lamari yana bukatar gamsasshiyar amsa, dole mu rike dokokin kasa da mutunta ta da kuma kishinta a kowane lokaci."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

- Podar Johnson Yiljwan

Rasha: Tinubu ya tura sako ga sojoji

Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an tsaro su cafke duk wanda suka gani dauke da tutar kasar Rasha a Najeriya.

Babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jarida bayan taron majalisar tsaro a Aso Villa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.