Ministan Buhari Ya Mayar da Martani Ga Bola Tinubu, Ya Goyi Bayan Zanga Zanga

Ministan Buhari Ya Mayar da Martani Ga Bola Tinubu, Ya Goyi Bayan Zanga Zanga

  • Tsohon ministan matasa da wasanni ya mayar da martani kan jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ranar Lahadi
  • Solomon Dalung ya bayyana cewa jawabin shugaban kasar bai da alaƙa da ƴan Najeriya don haka za su ci gaba da zanga-zanga
  • Wannan na zuwa ne yayin da zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnati mai ci ta shiga rana ta biyar yau 5 ga watan Agusta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Plateau - Tsohon ministan matasa da bunƙasa harkokin wasanni, Solomon Dalung ya caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kan zanga-zanga.

Dalung, wanda ya riƙe kujerar minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce jawabin Shugaba Tinubu ba zai tsaida zanga-zanga ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

Solomon Dalung da Bola Tinubu.
Ministan Buhari ya caccaki jawabin Bola Tinubu kan zanga-zanga Hoto: Solomon Dalung, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Punch ta tattaro cewa a jiya Lahadi, Bola Tinubu ya yi jawabi kai tsaye ga ƴan Najeriya inda a roƙi masu zanga-zanga su yi haƙuri su koma gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Solomon Dalung na ɗaya daga cikin waɗanda suka jaroranci zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu a ranar farko watau ranar Alhamis a Jos.

Tsohon Minista ya soki jawabin Tinubu

Da yake jawabi ga manema labarai a gaban dandazon masu zanga-zanga da suka ƙunshi musulmi da kiristoci, tsohon ministan ya ayyana jawabin Tinubu da fanko.

"Babu wani abu mai ma'ana a jawabin shugaban ƙasa, bai roƙi masu zanga zanga su yi haƙuri ba, ya dai yi masu barazanar cewa jami'an tsaro za su ci gaba da ɗaukar mataki.
"Jawabinsa bai da alaƙa da ƴan Najeriya, magana ya yi a kansa da muƙarrabansa. Duk kalaman da ya faɗi ba za su ƙara mana komai ba sai ƙwarin guiwar ci gaba da zanga-zanga."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

- Solomon Dalung.

Masu zanga-zangar dauke da tutar Najeriya, sun toshe tsohon shataletale da ke titin filin jirgin saman, inda suka tursasa wa motoci canza hanya a babban birnin Filato.

Masu zanga-zanga sun sake fitowa

A wani rahoton kuma masu gudanar da zanga-zanga a jihar Legas sun nuna jarumta bayan sake fitowa filin Ojota bayan 'yan daba sun fatattakesu

'Yan daba sun kori masu gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262