Zanga Zanga: Manyan 'Yan Siyasa da Kungiya da Suka Kushe Jawabin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najerita da safiyar jiya Lahadi 4 ga watan Agustan 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bola Tinubu ya yi jawabin ne yayin da ake cigaba da zanga-zanga saboda halin kunci da ake ciki a fadin kasar.
Mutane da dama a kasar sun kushe jawabin inda suka ce kwata-kwata bai yi magana kan bukatun masu zanga-zangar ba, cewar Punch.
Legit Hausa ta jero muku wandada suka yi magana kan jawabin Bola Tinubu a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Atiku Abubakar
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP a zabukan 2019 da 2023, Atiku Abubakar ya caccaki Bola Tinubu kan jawabin nasa.
Atiku na ganin babu wani abin da Tinubu ya fadi da ke da dangantaka da koken 'yan kasa a zanga-zangar da ake shiryawa.
2. Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya bukaci Bola Tinubu ya sake jawabi da zai magance matsalolin masu zanga-zanga.
Obi ya ce kwata-kwata Tinubu bai shirya shawo kan matsalolin da suke damun 'yan Najeriya ba.
3. Farfesa Wole Soyinka
Wole Soyinka ya accaki jawabin Bola Tinubu inda ya ce bai yi magana kan kisan mutane da aka yi ba a zanga-zanga.
Farfesa Soyinka ya bayyana cewa wannan ba lokacin harba harsashi tsakanin matasan da yunwa ta yiwa katutu ba ne, ya ce hakan zai kara jawo tashe-tashen hankula.
4. Femi Falana SAN
Fitaccen lauya a Najeriya, Femi Falana ya soki jawabin Shugaba Bola inda ya ce bai yi jawabin kai tsaye ga masu zanga-zanga da magana a kan matsalolinsu ba.
Femi Falana ya kara da nuna muhimmancin gwamnati ta yi kokarin magance rashawa a tsakanin wadanda ke bangaren man fetur.
5. Dele Momodu
Jigon PDP, Dele Momodu shi ma ya caccaki Bola Tinubu kan kin magana musamman game da bukatun masu zanga-zanga.
Momodu ya nuna damuwa kan shirin Tinubu na kawo sauyi a kasar duba da cigaba da ya samar lokacin mulkin Lagos.
6. Ajadi Oguntoyinbo
Jigon jam'iyyar NNPP shi ma ya nuna damuwa jawabin Tinubu game da rashin magana kan bukatun masu zanga-zanga a Najeriya.
7. Kungiyar Afenifere
Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi martani mai zafi ga shugaba Bola Tinubu kan maganganun da ya yi ga 'yan kasar.
Kungiyar ta ce akwai bukatar Bola Tinubu ya sake lura da maganar dawo da tallafin man fetur da ya jefa mutane cikin kunci.
Tinubu ya magantu kan dawo da tallafi
Kun ji cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan kiraye-kirayen dawo da tallafi a Najeriya yayin da ake zanga-zanga.
Tinubu ya ce babu maganar dawo da tallafin mai duk da ya sani ana cikin wani irin mawuyacin hali amma hakan ya zama dole.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng