Gwamna Ya Zargi Wasu Manyan Mutane da Ɗaukar Nauyin Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

Gwamna Ya Zargi Wasu Manyan Mutane da Ɗaukar Nauyin Zanga Zangar da Ake Shirin Yi

  • Gwamnan Katsina ya yi zargin akwai sa hannun wasu manyan mutane a zanga zangar da ake shirin yi kan taadar rayuwa
  • Malam Dikko Raɗda ya ce duk da mutane na da ƴanci amma yana ganin barin wannan zanga-zangar shi ya fi alheri ga mutane
  • Radda ya yi kira ga shugabanni a kowane mataki su ji tsoron Allah, su sauke nauyin amanar da al'umma suka ɗora masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radɗa ya yi zargin cewa wasu manyan mutane a kasar nan na da hannu a zanga-zangar da ake shirin yi.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce duk da mutane na da ƴancin yin zanga-zanga a kundin tsarin mulkin Najeriya, yana ganin barin ta a wannan lokacin zai fi zama alheri.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rufe makarantu, ya fara ɗaukar matakai kan zanga zangar da ake shirin yi

Malam Dikko Radda.
Gwamnan Katsina ya yi zargin akwai sa hannu wasu manya a zanga-zangar da ake shirin yi Hoto: Dr. Dikko Umaru Raɗda
Asali: Twitter

Malam Dikko Raɗɗa ya yi wannan furucin ne yayin wata hira ta musamman da TRT Hausa kan zanga-zangar da matasa ke shirin yi a watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya yarda ana cikin tsadar rayuwa

Idan ku na biye dai ƴan Najeriya musamman matasa sun shirya fita zanga-zanga kan tsadar rayuwa tsawon kwanaki 10 daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Yayin da aka tambaye shi kan kuken al'umma game da hauhawar farashi da tsadar rayuwar da suke ciki, Raɗɗa ya ce babu shakka ƴan Najeriya na cikin wahala.

Sai dai duk da haka mai girma gwamnan ya bayyana cewa abin da matasa ke tunanin yi na fita zanga-zanga ba shi ne maganin halin da ake ciki ba.

Ya ce ɗaya cikin matasan da suka fi zaƙewa ya faɗi wasu manyan mutane da ke ɗaukar nauyi, su na turo masu kudi don a yi zanga-zangar da za ta kifar da gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gana da masu shirin yin zanga zanga, ya shata layin da ba ya so a ƙetare

Gwamna Raɗɗa na zargn wasu manyan mutane

"Ƴan Najeriya suna da haƙkin yin zanga zanga su nuna damuwarsu kuma kundin tsarin mulki ya ba su dama, amma mu lura masu haɗa wannan zanga-zanga ba za su bar ƴaƴansu su fito.
"Kila ya taba yin shugabanci, a lokacin menene ya yi wa al'umma? Sannan idan wata dukiya gare shi ina ya same ta, ba dukiyar talakawa bace ba ko gado aka bar masa? Ya kamata mu lura."

- Dikko Radda.

Gwamnan ya yi kira ga shugabanni tun daga sama har kasa su rika fitowa suna yi wa mutane bayani na gaskiya kan yadda aka yi da dukiyarsu.

Kwamared Jamil Lawal, ɗaya ɗaga cikin masu shirya zanga-zanga a Ɗanja da ke jihar Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa za su fita kan tituna ba tare da tada hankali ba.

Matashin ya kuma tura ma wakilin mu tsarin da suka yi wanda ya ƙunshi toshe titin Malumfashi, wanda ya tafi har cikin birnin Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun saɓawa gwamna a Arewa, sun faɗi gaskiya kan zanga zangar da aka fara

"Babu tashin hankali ko ƙone-ƙone a zanga-zangar da za mu yi, tsarin mu shi ne kokenmu ya isa kunnuwan shugabanni kuma su ɗauki mataki.
"Za mu je sakatariyar ƙaramar hukuma, za mu tare titin da ya taso daga Zariya zuwa Malumfashi a daidai Marabar Dabai. Mun fahimci gwamnati ba ta fahimtar komai sai zanga-zanga," in ji shi.

Gwamnatin Tinubu ta karya farashin shinkafa

A wani rahoton na daban, an ji Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta fara share hawayen matasa game da tsadar rayuwa gabanin fara zanga zanga.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya ce babu sauran buƙatar zanga-zanga domin gwamnati ta fara magance damuwar matasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262