Sauya Sheka: Rukunin Mutane 3 da Suka Juyawa Abba Gida Gida da NNPP Baya a Watan nan
- Tafiyar siyasar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta samu koma baya sosai a watan Yulin shekarar nan ta 2024
- Nau'in kungiyoyi da shahararrun mutane akalla uku ne suka sauya sheka daga jami'yyar NNPP zuwa APC a jihar Kano
- A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku rukunin mutanen da suka sauya sheƙa suka bar tafiyar Abba Kabir Yusuf a Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tun kafin fara yakin neman zaben shekarar 2027 yan siyasa sun fara sauya sheka a jihar Kano.
Wasu kungiyoyin siyasa da yan wasan kwaikwayo da dama sun sauya sheka daga tafiyar jami'yyar NNPP zuwa APC a jihar Kano.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerin waɗanda suka fice daga tafiyar NNPP da Abba Kabir Yusuf ke jagoranta zuwa NNPP a watan Yulin da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Yan NNPP a Kura sun koma APC
A ranar 8 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ne wasu shugabannin jam'iyyar NNPP a karamar hukumar Kura suka fice daga NNPP zuwa APC a Kano.
Legit ta ta ruwaito cewa shugaban matasan jam'iyyar a Kura, Idris Musa ya bayyana cewa sun fita daga jami'yyar ne saboda ba a girmama su.
2. Jagoran NNPP a Shanono ya koma APC
A ranar 15 ga watan Yuli Legit ta wallafa cewa wasu jagororin NNPP a ƙaramar hukumar Shanono suka fice daga jami'yyar zuwa APC.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da haka tare da cewa za su girma jagoran mutanen mai suna Adamu Ciroma Koya.
3. Yan Kannywood sun fice daga NNPP
Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa a makon da ya wuce wasu jaruman Kannywood sun sauya sheka zuwa APC.
Cikin jaruman akwai Rabi'u Daushe, Babba Hikima, Hauwa Waraka, Alhaji Habu Tabule da sauransu.
'Dan takara ya fice daga NNPP
A wani rahoton, kun ji cewa jami'in tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kira na musamman ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Bashir Ahmad ya bayyana kuskuren da Abba Kabir Yusuf yake yi wajen gudanar da ayyuka a jihar Kano tare da faɗin mafita a garesa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng