Bola Tinubu Ya Shiga Taron FEC a Aso Villa Kwanaki 3 Gabanin Fara Zanga Zanga
- Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa kamar yadda aka saba a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya sun halarci taron na ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, 2024
- Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke fuskantar zanga-zangar da ƴan Najeriya suka shirya yi a watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Idan ba ku manta ba a taron FEC da ya gabata, majalisar ta umarci ministan kasafin kudi da tsare-tsare Atiku Bagudu, ya lalubo matakan da za a bu don ckke giɓin kasafin 2024.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, majalisar ta ba ministan wannan umarni ne domin samo mafita kan gibin da da za a samu a kasafin kudin bayan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau a taron, gwamnatin tarayya ta umarci a tura tirelolin shinkafa 740 zuwa jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja domin a rabawa masu karamin karfi.
Manyan gwamnati sun halarci FEC
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume sun halarci taron na yau Litinin, 29 ga watan Yuli, 2024.
Sauran kusoshin gwamnati da suka shiga zaman sun haɗa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da mai bada shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya da kusan duka ministoci da sauran mambobin FEC sun halarci taron yau a fadar shugaban ƙasa.
Legit Hausa ta fahimci cewa wannan taron na zuwa ne kwanaki uku gabanin ranar da ƴan Najeriya suka shirya fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Gwamnatin Tinubu na tsoron zanga-zanga
Ana da labari cewa yayin da aka hango hadarin zanga-zanga, a gurguje aka amince da kudirin mafi karancin albashi da wasu dabaru.
Wasu suna alakanta tabbatar da yancin kananan hukumomi da daukar aikin da ake shirin yi a NNPC da yunkurin hana matasa zanga-zanga.
Asali: Legit.ng