APC Ta Samu Gagarumar Matsala Bayan Manyan Jagororinta 500 Sun Koma PDP
- Jam'iyyar APC ta rasa manyan jagororinta guda 500 a jihar Cross Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
- Jagororin waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi bakwai na mazaɓar Sanatan Cross Rivers ta Kudu sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
- Shugaban masu sauya sheƙar ya bayyana cewa sun ɗauki matakin bayan sun samu gamsuwar cewa PDP ta fi APC mutuntaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Cross Rivers - Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Cross Rivers ta samu koma baya bayan wasu manyan jagororinta sun koma jam'iyyar PDP.
Kimanin jagorori 500 na jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi bakwai na mazaɓar Sanatan Cross Rivers ta Kudu suka tsallaka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagororin waɗanda suka juyawa APC bayan sun bayyana cewa sun fi gamsuwa da jam'iyyar PDP, cewar rahoton jaridar Leadership.
Meyasa suka bar APC zuwa PDP?
Shugaban masu sauya sheƙar kuma tsohon babban mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan jihar kan harkokin matasa, Mista Abel Bassey, ya ce sun yi nazari sosai kafin ɗaukar matakin da suka yi na barin APC.
Ya bayyana cewa sai da suka tsaya suka tantance tsakanin jam'iyyun inda daga ƙarshe suka fahimci cewa jam'iyyar PDP ta fi APC mutuntaka.
"Wannan ita ce ƙungiyar goyon bayana, 'Osopel Support Group' mun ɗauki kwakkwaran mataki domin sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP a hukumance."
"Kamar ɗan da ya bar iyayensa ya shiga garari daga baya ya fahimci kuskurensa, mun koma babbar jam'iyyarmu."
"Mun samu tarba daga jam'iyyar PDP, shugaban jam'iyyar na jiha da ɗaukacin shugabannin PDP na jihar Cross Rivers."
- Mista Abel Bassey
Ƴan majalisar PDP sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar dokokin jihar Kebbi guda uku da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Ƴan majalisar waɗanda su huɗu ne aka zaɓa a inuwar jam'iyyar PDP sun koma jam'iyyar APC ne tare da magoya bayansu.
Asali: Legit.ng