Ganduje Ya Tafka Asara Bayan Wasu Jiga Jigan APC Sun Koma PDP Ana Daf da Zabe

Ganduje Ya Tafka Asara Bayan Wasu Jiga Jigan APC Sun Koma PDP Ana Daf da Zabe

  • Ana daf da zabe, daruruwan magoya bayan jam'iyyun APC da LP ne suka watsar da jam'iyyunsu inda suka da koma PDP a jihar Edo
  • Magoya bayan jam'iyyun sun tabbatar da cewa sun yi haka ne domin goyon bayan dan takara wanda ba dan amshin shata ba
  • Wani dan APC a Gombe ya fadawa Legit Hausa cewa mafi yawan wadanda ke barin jam'iyyar son rai ne da rashin kishi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

JIhar Edo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jiga-jigan APC da LP sun watsar da jam'iyyunsu.

Daruruwan magoya bayan jam'iyyun APC da LP ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ana daf da zabe.

Kara karanta wannan

Kano: Siyasar Abba ta samu kalubale, fitattun yan Kannywood sun koma APC

'Ya'yan jam'iyyar APC sun koma PDP a jihar Edo
Daruruwan jam'iyyun APC da LP su n koma PDP a jihar Edo ana shirin zabe. Hoto: All Progerssives Congress, Peoples Democratin Party. Hoto: @OfficialPDPNig, @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

APC ta yi babban rashin mambobi zuwa PDP

'Ya'yan jam'iyyun sun koma PDP ne a jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024 yayin kamfen zabe, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamnan jihar a PDP, Asue Ighodalo da mataimakinsa, Osarodion Ogie ne suka karbi sabbin tuban.

Wadanda suka sauya shekar sun tabbatar da cewa sun zo PDP ne saboda cancanta da kwarewar dan takara Ighodalo.

'Yan APC da suka koma PDP suka ce sun watsar da dan takararsu ne saboda sun sani dan amshin shata ne sai abin da aka ce.

Kotu ta yiwa PDP illa a zaben Edo

Wannan na zuwa ne ana daf da gudanar da zaben gwaman jihar a watan Satumbar wannan shekara ta 2024 da muke ciki.

A kwanakin baya ne kotu ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da aka gudanar a watan Faburairun shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Bidiyon mazauna unguwannin jihar sun yi mubaya'a ga Aminu Ado

Yayin fidda gwanin ne dan takarar jam'iyyar Asue Ighodalo ya yi nasarar kasancewa wanda zai wakilce ta a zaben gwamna.

Wani dan APC a Gombe ya fadawa Legit Hausa cewa mafi yawan wadanda ke barin jam'iyyar son rai ne.

Mohammed Gimba ya ce ba su samu abin da suke so ba shi ne kawai musabbabin barinsu jam'iyyar.

"Daman ba kishin jam'iyya ko al'umma ne a gabansu ba, idan ana tafiya da su ko suna da mukami ba za su barta ba."

- Muhammad Gimba

Mataimakin gwamna, Shaibu ya koma APC

Kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP a jihar.

Shaibu ya dade da nuna sha'awar komawa APC wanda ya jima yana takun saka da Gwamna Godwin Obaseki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.