Kano: Siyasar Abba Ta Samu Kalubale, Fitattun Yan Kannywood Sun Koma APC
- A kwanan nan ana kara samun yan jam'iyyar NNPP A jihar Kano na cigaba da sauya sheka zuwa jami'yyar APC
- A wannan karon, wasu fitattun jaruman Kannywood sun kara ficewa daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma APC
- Jam'iyyar APC ta nuna maraba da shigowar jaruman ta kuma fadi yadda za su cigaba da aiki wajen cimma burinsu a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tafiyar siyasar gwamna Abba Kabir Yusuf ta jam'iyyar NNPP ta kara samun koma baya.
Hakan ya faru ne yayin da wasu shahararrun yan wasan Kannywood suka fita daga jam'iyyar NNPP zuwa APC a jihar Kano.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Kannywood da suka koma APC
A jiya Asabar, 27 ga watan Yuli, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa yan Kannywood da suka hada da Rabi'u Daushe sun koma APC.
Sauran fitattun yan wasan sun hada da Babba Hikima, Hauwa Waraka, Alhaji Habu Tabule da sauransu.
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya karbi tawagar jaruman ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a daren Juma'a.
APC ta yi maraba da yan Kannywood
A yayin karbar yan wasan, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa sun yi farinciki da dawowarsu APC wacce ita ce jam'iyya mafi girma a Afrika.
Sanatan ya ce samun mutane na sauya sheka zuwa APC a jihar Kano ya nuna yadda suke kara samun karɓuwa a wajen al'umma.
A karshe, Sanata Barau ya ce za su cigaba da aiki tare da jaruman Kannywood din har sai sun cika burinsu a jihar Kano.
Kano: Abba ya kaddamar da dasa bishiya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, mai girma Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin dasa miliyoyin bishiyoyi a fadin jihar.
Gwamnatin jihar Kano ta fadi dalilin fara dasa bishiyoyin da amfanin da al'ummar jihar za su samu daga aikin dasa itacen da Abba Kabir ya kaddamar.
Asali: Legit.ng