Ganduje Ya Sake Yiwa PDP Lahani, 'Yan Majalisa 3 Sun Koma APC

Ganduje Ya Sake Yiwa PDP Lahani, 'Yan Majalisa 3 Sun Koma APC

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kebbi ta yi gamu da babban koma baya a siyasar jihar ta yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • PDP ta samu koma bayan ne bayan uku daga cikin ƴan majalisar ta guda huɗu sun watsar da laima sun rungumi tafiyar jam'iyyar APC
  • Shugaban majalisar dokokin jihar wanda ya sanar da shigowarsu APC, ya ce sun ɗauki matakin ne bayan sun gamsu da kamun ludayin mulkin Gwamna Nasir Idris

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Ƴan majalisar dokokin jihar Kebbi guda uku da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Ƴan majalisar waɗanda su huɗu ne aka zaɓa a inuwar jam'iyyar PDP sun koma jam'iyyar APC ne tare da magoya bayansu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jigon APC ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

'Yan majalisa sun koma APC a Kebbi
'Yan majalisar PDP sun sauya sheka zuwa APC a Kebbi Hoto: @OfficialAPCNg, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Ƴan majalisar PDP sun koma APC

Shugaban majalisar dokokin jihar, Usman Yankwai ya sanar da shigowarsu jam'iyyar a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ƙananan hukumomi na jam'iyyar a ƙaramar hukumar Koko Besse, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa sun sauya sheƙar ne saboda gamsuwa da salon mulkin gwamnan jihar, Nasir Idris.

Usman Yankwai ya bayyana cewa ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun fito ne daga mazaɓun Argungu, Bunza da Yauri, rahoton VMT News ya tabbatar.

Yayin da yake maraba da ƴan majalisar zuwa APC, shugaban jam'iyyar na jihar, Abubakar Kana Zuru ya nuna jin daɗinsa kan matakin da suka ɗauka.

Ya ba su tabbacin cewa jam'iyyar za ta ba su goyon baya tare da yi musu adalci.

Ya bayyana matakin Gwamna Nasir Idris na kawo ci gaba a jihar cikin shekara ɗaya, ya ɗauke shi ne saboda inganta rayuwar mutanen jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Jam'iyyar APC ta dauki muhimmin mataki

APC za ta ƙwace Edo - Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Edo na shekarar 2024.

Ganduje ya bayyana jin daɗinsa kan sauya sheƙar da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya yi zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu kaso 50% na ƙuri'un jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng