Gwamnan APC Ya Gabatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ga Bola Tinubu
- Gwamnan Imo kuma shugaban gwamnonin APC ya jagoranci Anyim Pius Anyim zuwa wurin Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa
- Hope Uzodinma ya gabatar da tsohon shugaban majalisar dattawan ga Tinubu bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC ranar Laraba
- Da yake jawabi bayan ganawar, gwamnan ya ce mafi akasarin mutane na godiya ga Tinubu bisa ayyukan da yake yi a Kudu maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya gabatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Idan ba ku manta ba Anyim Pius Anyim, tsohon sakataren gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Sanata Anyim ya koma APC ne tare da wasu magoya bayansa a babban taron rufe kamfen jam’iyyar APC na karamar hukumar Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sakamakon haka ne Uzodinma, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC ya jagoranci Pius Anyim zuwa wurin Tinubu yau Laraba.
Vanguard ta rahoto cewa Shugaba Tinubu ya yi wa tsohon shugaban majalisar dattawan barka da zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Uzodinma ya yabawa Bola Tinubu
Da yake jawabi ga masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Uzodinma ya yabawa gwamnati mai ci bisa tallafawa al'ummar Kudu maso Gabas.
Ya ce kungiyar gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas tana jin daɗin jagorancin shugaban ƙasa kuma tana ƙara godiya bisa ayyukan da yake zubawa al'ummar yankin.
A ruwayar The Nation, Uzodinma ya ƙara da cewa kwanan nan wata ƙaramar hukuma guda ta dawo inuwar APC duk saboda ayyukan alherin da wannan gwamnatin ke yi.
"Mun shigo sabon babi kuma mutane da dama sun yarda cewa gwamnati mai ci tana aikin da ya dace," in ji Uzodinma.
A nasa jawabin Sanata Anyim ya ce Najeriya ce a zuciyarsa, "domin akwai buƙatar mu haɗa hannu wuri ɗaya domin ci da ƙasar nan zuwa gaba."
Kusoshin gwamnatin Tinubu sun gana a Aso Villa
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta tashi tsaye a kokarin daƙile yunkurin da matasa ke yi na hawa kan tituna a watan Agustan nan.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya shiga taron gaggawa da Nuhu Ribadu da ministocin kasa kan batun zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng