Tinubu Na Kokarin Lallaba Matasa, Zanga Zanga Ta Barke a Abuja Kan Tsige Ndume

Tinubu Na Kokarin Lallaba Matasa, Zanga Zanga Ta Barke a Abuja Kan Tsige Ndume

  • Kungiyar matasa a jihar Borno sun gudanar da zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja kan tsige Sanata Ali Ndume da majalisa ta yi
  • Matasan sun gudanar da zanga zangar ne a dandalin Unity Fountain inda suka bayyana buƙatarsu ga shugaban majalisar dattawa
  • Majalisar dattawan Najeriya ta tsige Sanata Ali Ndume ne daga matsayinsa na mai tsawatarwa kan magana da ya yi ga Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata kungiyar matasan cigaban kudancin Borno ta yi zanga zanga a Abuja kan tsige Ali Ndume.

A yau Laraba, 24 ga watan Yuli ne matasan suka taru a dandalin Unity Fountain domin nuna kin amincewarsu da matakin da majalisar ta dauka.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya yi magana kan batun zanga zangar matasa, ya kawo mafita 1

Ali Ndume
Ana zanga zanga kan tsige Ali Ndume a Abuja. Hoto: Senator Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matasan sun tura buƙata ta musamman ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Tsige Ali Ndume a majalisa

Sanata Ali Ndume ya mika korafi ne ga shugaban kasa Bola Tinubu kan wahalar rayuwa da talakawa ke ciki a Najeriya.

Biyo bayan haka jami'yyar APC ta bukaci a tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa a majalisa wanda majalisar ta tabbatar da hakan.

Buƙatar masu zanga zangar Ndume

Shugaban masu zanga zangar, Mohammed Ibrahim Biu ya ce Sanata Ali Ndume mutum ne mai nagarta sosai.

A cewar Mohammed Ibrahim saboda haka ne suka fito zanga zanga domin bukatar Sanata Godswill Akpabio ya mayar da shi mukaminsa.

Ibrahim: 'Babu gaskiya kan tsige Ndume'

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Muhammad Ibrahim ya koka kan cewa bai kamata a cire mutum daga mukaminsa ba bayan ya fadi gaskiya.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote: Majalisa ta dauki mataki ganin an samu sabani da gwamnatin tarayya

Ya kuma kara da cewa an tsige Ali Ndume ne saboda son zuciya ba domin kawo cigaba a Borno ko Najeriya ba.

Ndume ya ki karbar sabon mukami

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ki karɓar sabon naɗin da aka yi masa a majalisa.

Sanatan ya ƙi karɓar sabon muƙamin da shugaban majalisar ya ba shi na shugaban kwamitin harkokin yawon buɗe ido.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng