Abinci Ya Kare: Gwamna Ya Kori Duka Shugabannin Kananan Hukumomi, Ya Ba da Umarni

Abinci Ya Kare: Gwamna Ya Kori Duka Shugabannin Kananan Hukumomi, Ya Ba da Umarni

  • Mai girma Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya kori dukan shugabannin riko na kananan hukumomi baki daya
  • Matakin na zuwa ne bayan wa'adin zababbun shugabannin rikon na ƙananan hukumomi ya kare a watan Faburairun 2024
  • Wasu na ganin matakin bai rasa nasaba da hukuncin Kotun Koli na ba kananan hukumomi ƴancin kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Gwamnatin Kebbi ta sallami dukkan shugabannin riko na ƙananan hukumomi 21 a jihar.

Gwamna Nasir Idris ya dauki wannan mataki tare da umartansu da su mika ragamar ƙananan hukumomin ga daraktocin ma'aikatasunsu.

Gwamna ya kori shugabannin kananan hukumomi 21
Gwamna Nasir Idris ya sallami shugabannin kananan hukumomi 21 a jihar Kebbi. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Twitter

Kebbi: Gwamna ya ba korarrun ciyamomi umarni

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mukaddashin babban sakataren ma’aikatar, Aliyu Hassan Kalgo ya fitar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya kafa tarihi, ya ƙirkiro doka kan mata masu iddah a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalgo ya ce matakin rushe shugabannin ƙananan hukumomn zai fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.

Ya umarci korarrun shugabannin riko na ƙananan hukumomin su mika ragamar gudanar da ofisoshinsu da daraktocin gudanarwar kananan hukumominsu.

Wannan na zuwa ne bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar a watan Fabrairun 2024, Aminiya ta tattaro.

Za a gudanar da zaɓen kananan hukumomi

Ana hasashen matakin bai rasa nasaba da hukuncin Kotun Koli da ya ba wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kansu.

Bayan hukuncin ne jam’iyyun adawa da kungiyar (IPAC ) suka bukaci a rushe shugabanninsu riƙon domin gudanar da wani zabe a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar zaben jihar (KESIEC) ta shirya gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a ranar 31 ga watan Agusta 2024.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, gwamnatin Kano za ta gudanar da zaben kananan hukumomi

Gwamnan Kwara ya kori shugabannin ƙananan hukumomi

A baya kun ji cewa gwamnatin jihar Kwara ta kori dukkan shugabannin kananan hukumomi har 16 da ke fadin jihar baki daya.

Jihar ta yi godiya ga dukkan shugabannin kananan hukumomin inda ta yaba musu kan jajircewa da tabbatar da kawo cigaba.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.