Amaechi: Tsohon Gwamna Ya Tattara Kayansa Ya Fice Daga APC? Jam’iyyar Ta Magantu
- APC a jihar Ribas ta ce ta gaza tantance ko Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufurin jiragen sama yana jam’iyyar ne ko ya fita
- Tony Okocha, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC a Rivers, ya ce tsohon gwamnan ya nesanta kansa da harkokin jam'iyyar
- An ruwaito cewa Amaechi ne da kansa ya gargadi shugabannin jam’iyyar da su daina aika masa da sakonnin da suka shafi al’amuran APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Port Harcourt, Ribas – Shugabannin jam’iyyar APC a jihar Ribas ba su da tabbas game da jam'iyyar da Rotimi Amaechi yake ciki a halin yanzu.
Tony Okocha, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar a Rivers, ya ce tsohon gwamnan ya nesanta kansa da APC.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Okocha ya ba da wani labari inda Amaechi ya tsawatarwa sakataren jam’iyyar na jihar kan gayyatarsa wajen taron masu ruwa da tsaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okacha ya yi ikirarin cewa Amaechi ne da kansa ya gargadi shugabannin APC da ka da su sake aikz masa da takardar gayyatar al’amuran jam'iyyar.
Abin da APC ta ce game da Amaechi
Okocha ya bayyana rashin tabbas game da matsayin Amaechi, inda ya bayyana janye jikinsa bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa da kuma kin halartar tarurrukan jam’iyyar.
Ya kuma yi nuni da cewa ba shi ne ya kamata a tambaya game da jam'iyyar siyasar Amaechi ba tunda a yanzu tsohon gwamnan ya yanke alakarsa da APC, inji rahoton The Nation.
Amaechi wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Ribas har na wa'adi biyu kafin ya zama minista, ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 amma ya sha kaye a hannun shugaba Bola Tinubu.
Makusantan Amaechi sun fice daga APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta rasa wasu manyan jiga-jiganta da ke da kusanci da tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi a lokacin zaben 2023.
Fitar Princewill Dike daga APC da komawarsa PDP ya bawa mutane da dama mamaki saboda an san yana daya daga cikin hadiman tsohon gwamna Amaechi na kut-da-kut.
Asali: Legit.ng