Ganduje Ya Gurgunta Shirin Obi, Sanatan Jam’iyyar Labour Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Ganduje Ya Gurgunta Shirin Obi, Sanatan Jam’iyyar Labour Ya Sauya Sheka Zuwa APC

  • Salon shugabanci da dabarun tafiyar da APC da Abdullahi Ganduje ke yi na ci gaba da jawo ra'ayin manyan 'yan siyasa ga jam'iyyar
  • A yau Talata, sanata mai wakiltar Imo ta Gabas Ezenwa Onyewuchi, ya fice daga jam'iyyar Labour tare da komawa APC mai mulki
  • Ana ganin wannan babban rashin da jam'iyyar Labour ta yi, zai iya kawo tangarda ga kudurin siyasar Peter Obi a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata mai wakiltar Imo ta Gabas kuma dan jam’iyyar Labour, Ezenwa Onyewuchi, ya koma jam’iyya mai mulki a kasa ta APC.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Onyewuchi a zauren majalisar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamna a Arewa, ta buƙaci ya baro PDP

Sanata Ezenwa Onyewuchi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Sanatan Labour, Ezenwa Onyewuchi ya sauya sheka zuwa APC. Hoto: @EzenwaOnyewuchi
Asali: Facebook

Hope Uzodimma, gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin Progressives Forum (PGF) na cikin zauren lokacin da aka karanta wasikar, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan LP ya koma jam'iyyar APC

Sanatan na Imo ya dogara ne da sashe na 68 (1g) na kundin tsarin mulki yayin da ya yanke shawarar sauya shekarar daga jam'iyyar Peter Obi zuwa ta Abdullahi Ganduje.

"Wannan hukuncin ya biyo bayan rabewar kai da rikicin da ya ta'azzara a jam'iyyar Labour waddda na samu nasarar zabena zuwa majalisar dattawan Najeriya."
“Wannan matakin ya zama dole dogaro da sashi na 68(1g) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
"Jihar Imo da dukkan yankin kudu maso Gabas na cigaba da zama cikin haɗin kai a ƙarƙashin shugabancin gwamnanmu mai ƙwazo, Hope Uzodimma."

- A cewar wasikar.

Kara karanta wannan

Edo 2024: PDP ta fusata bayan mataimakin gwamna ya fice daga jam'iyyar zuwa APC

Jaridar The Nation ta ruwaito Akpabio ya umarci sajan din majalisar dattawa da ya baiwa Sanata Onyewuchi sabon wurin zama a ɓangaren 'yan majalisa masu rinjaye.

A halin yanzu yawan sanatoci daga jam'iyyar Labour Party a majalisar sun tsaya a biyar.

PDP ta fusata da sauya shekar Shaibu

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa jam'iyyar PDP ta nuna tsananin fushinta kan yadda mataimakin gwamnan jihar Edo ya koma jam'iyyar APC.

Jam'iyyar ta ce lamarin son kansa da zagon kasansa ya fito fili kuma su ne za su lashe zaben da za a yi na gwamnan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.