'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Tona Inda Tinubu Yake Kwaso 'Tsarin Gallazawa Talaka'

'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Tona Inda Tinubu Yake Kwaso 'Tsarin Gallazawa Talaka'

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan zanga zanga
  • Adewole Adebayo ya ce Bola Tinubu da kansa ya jagoranci zanga zanga a lokacin mulkin shugaba Goodluck Ebele Jonathan
  • Haka zalika, Adewole Adebayo ya bayyana matsayarsa kan shiri zanga zangar da matasa ke shirin yi a dukkan jihohin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP ya yi magana kan zanga zanga da ake shirin yi a Najeriya.

Adewale Adeniyi ya ce Bola Tinubu da kansa ta jagoranci zanga zanga kuma yanzu kamar za a rama abin da ya yi a lokacin Goodluck Jonathan ne.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 10 ayi zanga zanga, Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU

Bola Tinubu
An caccaki Tinubu kan cire tallafin man fetur. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Adewole Adebayo ya fadi hanyar da matasa za su bi wajen kawo sauyi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi zanga zanga a baya

Dan takara a jam'iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo ya ce Tinubu da Muhammadu Buhari sun yi zanga zanga kan cire tallafin man fetur a baya.

Adewole Adebayo ya ce Tinubu ya yaki Jonathan kan biyewa IMF wajen cire tallafin mai amma abin takaici shi ya cire tallafi ta hanyar da ta jawo gallazawa al'umma.

Har ila yau, Adewole ya ce yanzu haka Tinubu ya zama ɗan amshin shatar hukumar IMF da bankin duniya duk da cewa shi yake nuna adawa da su a baya.

Matsayar Adewole kan zanga zanga

Adewole Adebayo ya bayyana cewa yana dar dar kan wadanda suke shirya zanga zangar da ake son yi a ranar 1 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Peter Obi: 'Yan adawa sun tona abin da Tinubu yake shiryawa masu zanga zanga

Dan takarar shugaban kasar ya ce maimakon zanga zangar da za ta iya kai wa ga matsala kamata ya yi a mayar da hankali kan zabe mai zuwa.

Ya ce ya kamata matasa su rika bude idonsu a lokutan zabe domin tabbatar da cewa ba zaben tumun dare suka yi ba, rahoton Vanguard.

Ahmed Lawan ya tura sako ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da al'ummar Najeriya ke kara shiga kuncin rayuwa saboda tsadar kayayyaki, Sanata ya tura sako ga Bola Tinubu.

Sanata Ahmed Ibrahim Lawan daga jihar Yobe ya bayyana halin da ake ciki a Najeriya da kuma abin da ya kamata shugaban kasa ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng