Ganduje Ya Sake Yi Wa Jam'iyyu 2 Lahani, Wasu Jiga Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ganduje Ya Sake Yi Wa Jam'iyyu 2 Lahani, Wasu Jiga Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun ta rasa wasu manyan kusoshinta waɗanda suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
  • Rahotanni sun bayyana cewa ƴaƴan PDP da ADP sama da 100 sun fice daga jam'iyyunsu zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • Masu sauya sheƙa daga PDP karkashin jagorancin tsohon sakataren ƙaramar hukuma, Alimi Surajudeen sun ɗauki mataki ne saboda an maida su saniyar ware

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Wasu jiga-jigai da mambon jam'iyyun PDP da ADP a jihar Osun sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC jiya Lahadi 21 ga watan Yuli, 2024.

Gomman masu sauya shekar sun fito ne daga yankin ƙaramar hukumar Irewole a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, daruruwan 'yan adawa sun dawo cikinta a Kaduna

Oyetola da Gwamna Adeleke.
Jam'iyyar APC ta karɓi ɗaruruwan mambobin PDP da ADP a Osun Hoto: Senator Nurudeen Jackson, Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Masu sauya sheƙar karkashin jagorancin tsohon sakataren ƙaramar hukumar Alimi Surajudeen sun kafa hujjar cewa an maida su saniyar ware shiyasa suka bar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa jiga-jigan PDP suka koma APC?

Kamar yadda Vanguard ta tattaro, Sarajudeen ya caccaki jam'iyyar PDP karkashin Gwamna Ademola Adeleke bisa fifita ƴan uwansa da abokansa fiye da waɗanda suka yi wahala.

"Abin takaici ne ka zauna a jam'iyya, ka yi aiki tukuru amma daga karshe a yi watsi da kai. Jam'iyyar ta koma hannun ƴan dangi da abokai, ba ruwansu da wane hali mambobi ke ciki.
"Ba zan iya ci gaba da zama a irin wannan jam'iyyar ba," in ji shi.

Jam'iyyar APC ta fara shirin 2026

Da yake jawabi kan ci gaban, Manajan Darakta na hukumar kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa, Bola Oyebanji, ya yiwa masu sauya sheƙar barka da zuwa.

Kara karanta wannan

Edo 2024: PDP ta fusata bayan mataimakin gwamna ya fice daga jam'iyyar zuwa APC

Ya ce wannan sauya sheƙa na ƙara nuna yadda jam'iyyar APC ke ƙara yaɗuwa kuma ta shirya dawowa kan madafun iko a jihar Osun a zaɓen 2026, The Nation ta rahoto.

“Tun da muka bar gwamnati, APC karkashin jagorancin Adegboyega Oyetola ta ƙara tsayuwa kan ƙafafunta.
"Babu daya daga cikin mambobinmu da ya koma wata jam’iyya, kuma a yau, muna maraba da mambobi 120 daga PDP, ADP zuwa APC,” inji Oyebamiji.

APC ta karbi masu sauya sheƙa a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa Mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Masu sauya sheƙar su 702 sun sauya sheƙar ne a mazaɓar Makera da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262