Dan Majalisar APC Ya Gwangwaje Ɗiyarsa da Kyautar Dalleliyar SUV Bayan Gama Sakandare
- Hon. Yusuf Gagdi ya gwangwaje ɗiyarsa matashiyar budurwa da kyautar motar ƙirar Lexus RX bayan kammala sakandare
- AIsha Yusuf Gagdi ta gama makarantar sakandare tare da samun sakamako mai kyau a jarabawar shiga jami'a kamar yadda aka gano
- Wannan kyautar motar miliyoyi na zuwa ne yayin da ake tsaka da matsi da yunwa a faɗin Najeriya, lamarin da ya janyo cece-kuce
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan majalisar mai wakiltar mazaɓar Pankshin/ Kanke/Kanam ta tarayya, Yusuf Gagdi, ya siyawa diyarsa sabuwar mota ƙirar Lexus RX domin taya ta murnar kammala sakandare.
Diyar ɗan majalisar ta gama karatunta na sakandare tare da samun maki mai kyau a jarabawar shiga jami'a.
Budurwar mai suna Aisha Gagdi, ta kammala karatun sakandare ne a makarantar Lead British International School Abuja, ranar Asabar, kamar yadda Gagdi ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan majalisar ya ce:
"A yau, na halarci bikin kammala makaranta na ɗiyata. Ganinka ɗiyata da nake so tana ratsa matakai ya cika zuciyata da tsananin alfahari da ƙauna"
A wannan wallafar da dan majalisar ya yi, bai saka hotuna ko yin bayani game da motar da ake zargin ya sayawa diyar tasa ba.
Hotunan dalleliyar motar ya yadu
Sai dai wani ma'abocin amfani da sahar Facebook mai suna Saminu Maigoro, ya wallafa hoton matashiyar tare da mahaifinta a cikin sabuwar motar da ya saya mata.
“Ina taya ki murna Aisha Yusuf Gagdi, da kammala karatunki daga Lead British International School, Abuja. Ina fatan ya zama farko rayuwarki zuwa nasara.
"Domin taya murnar kammala karatunta da kuma ƙwazonta a JAMB, mahaifinta ya gwangwajeta da kyautar mota."
- A cewar Maigoro.
Kalli zafafan hotunan motar a kasa:
Kyautar motar ta jawo cece-kuce
Wasu 'yan soshiyal midiya sun taya Aisha murnar kyautar motar, yayin da wasu suka caccaki ɗan majalisar kan wannan kyautar duba da halin matsin da ake ciki a ƙasar.
Wani mai amfani da sahar mai suna Kamardeen Ibrahim Umar ya ce:
"Ina taya ta murna, amma ta yaya zamu cigaba a matsayinmu na ƙasa kamar haka. Akwai 'ya'yan marasa galihu da ke ƙoƙarin biyan kudin JAMB, WAEC ko NECO, wasu kuma ba su da kudin zuwa jami'a.
"A ɗaya ɓangaren kuma, 'yan siyasa mutane suka zaɓa suna sacewa da raba albarkatun ƙasa tsakaninsu domin morewa tare da gwangwaje iyalansu. Mu haɗu mu kawo ƙarshen shuganci mara kyau a Najeriya."
'Yan majalisa sun sadaukar da rabin albashinsu
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa 'yan majalisar Najeriya sun sha caccaka da suka bayan da suka rage rabin albashinsu.
Sun sanar da cewa daga nan zuwa watanni shida za su dinga karbar rabin kudin albashin, lamarin da ya janyo suka da cece-kuce daga jama'a.
Asali: Legit.ng