Ganduje Ya Shirya Kwace Kujerar Gwamna Daga Hannun PDP, Ya Lissafo Hanyoyi 3

Ganduje Ya Shirya Kwace Kujerar Gwamna Daga Hannun PDP, Ya Lissafo Hanyoyi 3

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta kayar da PDP a zaɓen gwamna da za a yi a jihar Edo
  • Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan na watan Satumba
  • A cewar Ganduje, APC ta samu kaso 50% cikin 100% na ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen mai zuwa, saboda dawowar mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Edo na shekarar 2024.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen na ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers kuma yana da burin ƙwato jihar daga hannun jam’iyyar PDP a zaɓen da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fara zawarcin mataimakin gwamnan PDP, za ta kafa tuta a ofishinsa

Ganduje ya sha alwashin kwato jihar Edo
Ganduje ya shirya kwato jihar Edo daga hannun PDP Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ganduje ya bayyana abubuwa guda uku da APC za ta iya yi domin kayar da jam’iyyar PDP mai mulki a jihar mai arziƙin man fetur, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dawowar Shaibu za ta tabbatar da nasarar APC

Ganduje ya bayyana jin daɗinsa kan sauya sheƙar da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya yi zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu kaso 50% na ƙuri'un jihar.

Mataimakin gwamnan wanda aka mayar kan muƙaminsa ya koma jam’iyyar APC ne a ranar Asabar, 21 ga watan Yuli, jim kaɗan bayan ya tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin kashe shi da aka yi.

Halartar Tinubu a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe

Ya bukaci kwamitin yaƙin neman zaɓen da ya tattaro mambobin jam'iyyar a ƙananan hukumomi da mazaɓu domin gudanar da yaƙin neman zaɓe tare da kaɗa ƙuri'a, rahoton jaridar Gazettengr ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun goyi bayan NLC, sun faɗi matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi

An shirya wani babban gangami, wanda Shugaba Bola Tinubu zai halarta, domin fara yaƙin neman zaɓen.

Ɗan takarar APC yana da tsari

Ganduje ya yabawa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebolo, da abokin takararsa, Dennis Idahosa, kan yadda suke da tsarin ci gaban jihar Edo.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗa jihar Edo da gwamnatin tarayya domin samun romon dimokuraɗiyya, wanda za a samu ta hanyar zaɓen ƴan takarar APC.

Ganduje ya karɓi Shaibu zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya watsar da jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi mataimakin gwamnan a hukumance zuwa cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng