Tsohon Shugaban PDP Ya Fusata da Yadda Wasu Ke 'Satar' Kudi, Ya Fice Daga Jam'iyyar
- Tsohon shugaban PDP reshen jihar Ondo, Ebenezer Alabi ya sanar da ficewa daga jam'iyyar bisa wasu dalilai ana shirin zaɓen gwamna
- Alabi ya bayyana cewa ba zai ci gaba da zama a jam'iyyar da jagororinta ba su da buri face su kwashe kuɗin kamfen da aka turo
- Ya bayyana cewa ya yanke shawarar tattara kayansa ya bar PDP bayan tattaunawa da iyalai, ƴan uwa da abokan arziki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar adawa PDP reshen jihar Ondo ya buɗe sabon shafi a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a 2024.
Rahotanni sun bayyana tsohon shugaban PDP na jihar, Ebenezer Alabi, ya sanar da ficewa daga jam'iyyar.
Mista Alabi ya riƙe kujerar shugaban jam'iyyar PDP a jihar Ondo a lokacin mulkin tsohon gwamna marigayi Olusegun Agagu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Alabi ya fice daga PDP?
Ya bayyana cewa ya yanke shawarin jefar da kwallon mangoro domin ya huta da ƙuda bayan tuntubar iyalansa, abokanan siyasa da abokanan arziƙi.
Ebenezer Alabi ya ce ba zai iya ci gaba da zama a jam'iyyar da jagororinta ba su da wani buri face su samu dama su tara kudi a lokacin zaɓen da ke tafe a jihar.
Hakan na ƙunshe ne a wasiƙar ficewa daga PDP da tsohon shugaban ya rubuta mai ɗauke da kwanan watan 18 ga Yuli, 2024.
A rahoton The Nation, Alabi ya ci gaba da cewa:
"Kuɗaɗen da aka turo domin kamfe a babban zaben da ya wuce sun kare ne a aljihunan waɗannan shugabanni waɗanda suka zama silar rashin nasarar PDP."
Alabi ya ɗauki wannan mataki ne sa’o’i 24 bayan da wasu jiga-jigai da ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka fice daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
APC ta mayar da martani ga PDP
Kuna da labarin jam'iyyar APC ta yi zazzafan martani ga PDP biyo bayan maganganu da gwamnonin jam'iyyar suka yi bayan kammala wani taro.
A jiya Alhamis, jami'in yada labaran APC, Barista Felix Morka ya yi martanin inda ya ce PDP ba ta da wani hurumin zarginsu a Najeriya.
Asali: Legit.ng