Kaduna: Jigon APC Ya Yi Martani Bayan Cin Mutuncin Dan Bilki Kwamanda, Ya Ba da Shawara

Kaduna: Jigon APC Ya Yi Martani Bayan Cin Mutuncin Dan Bilki Kwamanda, Ya Ba da Shawara

  • Jigon APC a jihar Kaduna mai suna Yusuf Ali ya magantu kan cin zarafin Abdulmajeed Dan Bilki Kwamanda
  • Yusuf Ali ya ce kwata-kwata a tsarin jam'iyyar APC ba su yadda haka ba inda ya ce Najeriya mulkin dimukradiyya take
  • Jigon jam'iyyar ya bukaci a kaddamar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu game da cin zarafin Kwamanda

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Yusuf Ali ya yi Allah wadai da cin zarafin Abdulmajeed Dan Bilki Kwamanda.

Yusuf Ali ya ce kowane dan Najeriya yana da 'yancin fadin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ko fargaba daga hukuma ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah, kungiyar makiyaya ta yi kira ga mutanenta

Jigo APC ya yi Allah wadai da cin mutuncin Dan Bilki Kwamanda a Kaduna
Jigon APC, Yusuf Ali ya bukaci daukar mataki kan cin zarafin Dan Bilki Kwamanda. Hoto: Yusuf Ali.
Asali: UGC

Dan Bilki Kwamanda: Jigon APC ya yi Allah wadai

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jigon jam'iyyar ya fitar wanda Legit ta samu a jiya Alhamis 18 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata shugabannin siyasa su sani ana mulkin dimukradiyya ne ba na mulkin soja ko kuma kama-karya ba, cewar TheCable.

Har ila yau, Yusuf ya bukaci Amurka da Burtaniya da kasashen Turai su dauki mataki kan 'yan siyasa wurin hana su fasfo na shiga kasashensu.

Jigon jam'iyyar ya ce hakan zai yi matukar taimakawa wurin tabbatar da bin tsarin dimukaradiyya da kare hakkin mutane.

An bukaci kaddamar da bincike kan Kwamanda

"Ina son kara tunawa shugabannin siyasa cewa Najeriya ba a karkashin mulkin soja ko kama-karya muke ba."
"Jam'iyyar APC ta himmatu wurin tabbatar da bin doka da kuma kare hakkin al'umma a kasar."

Kara karanta wannan

Kano: Bayan naɗa sarakuna 3, Gwamna Abba Kabir ya baiwa Sarkin Gaya takarda

"APC ta samar da yanayi mai kyau inda kowa zai fadi albarkacin bakinsa ba tare da tsoron komai ba."

- Yusuf Ali

Yusuf ya bukaci kaddamar da bincike kan lamarin tare da tsayawa Dan Bilki Kwamanda musamman wadanda suka ki jinin cin zarafin al'umma.

Gwamna ya magantu kan cin zarafin Kwamanda

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta barranta kanta game da cin zarafin Dan Bilki Kwamanda da aka yi.

Gwamna Uba Sani ya yi Allah wadai da lamarin inda ta bukaci kaddamar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.