El Rufa’i: Jagoran Yakin Zaben Tinubu Ya Fadi Yadda APC Ta Dauko Hanyar Wargajewa

El Rufa’i: Jagoran Yakin Zaben Tinubu Ya Fadi Yadda APC Ta Dauko Hanyar Wargajewa

  • Manya a APC sun fara magana kan yadda ake samun sabani tsakanin wadanda suka taya shugaba Bola Tinubu yakin neman zabe
  • Daya daga cikin wanda suka jagoranci yakin neman zaben shugaba Bola Tinubu, Jesutega Onokpasa ne ya yi magana kan lamarin
  • Jesutega Onokpasa ya bayyana matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kamata ya ɗauka domin dinke APC waje guda a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC, Jesutega Onokpasa ya nuna fargaba kan yadda aka fara nuna wariya ga wasu manya a jam'iyyar.

Jesutega Onokpasa ya yi magana ne kan yadda APC mai mulki ta ke son juya baya ga Alhaji Yahaya Bello da Malam Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jigon APC ya yi martani bayan cin mutuncin Dan Bilki Kwamanda, ya ba da shawara

Jam'iyyar APC
Jigo a APC ya koka kan nuna wariya ga manyan jam'iyya. Hoto: Kola Sulaimom.
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Jesutega Onokpasa ya ce ya fadi maganganun ne da nufin kawo gyara tun kafin lokaci ya kure ga jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Korafin Jesutega a kan taba jagororin APC

Jesutega Onokpasa wanda daya ne daga cikin wadanda suka jagoranci yakin neman zaben Bola Tinubu ya ce an fara nuna wariya a tafiyar jam'iyyar.

Jigon APC ya bayyana cewa Nasir El-Rufai ya yi aiki sosai wajen ganin samun nasarar Tinubu amma yanzu haka ana masa bita da kulli.

Har ila yau ya koka kan yadda jam'iyyar APC ta ke kallo EFCC na wulakanta Yahaya Bello da sunan shari'a a kotu.

Jesutega: 'Ya kamata APC ta sake zama'

Jesutega Onokpasa ya ce bai kamata APC ta rika yakar kanta da kanta ba a halin yanzu, rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An fadawa Tinubu sirri 3 domin shawo kan talakan Najeriya cikin sauki

Jigon ya ce akwai bukatar shugabannin jam'iyyar su sake tunani kan yadda lamura ke tafiya domin kawo gyara da zai kai ga nasara a gaba.

Ya ce matuƙar APC ta zuba ido aka cigaba da wulakanta wadanda suka sha wahala a tafiyar to lallai jam'iyyar za ta wargaje.

APC ta wargaje gida uku a Zamafara

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin jam'iyyar APC ya kara ƙamari a jihar Zamfara yayin da aka kara samun tsagin da ya ɓalle daga uwar jam'iyyar.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Sani Jaji ya ware shi da mutanensa saboda zargin nuna musu wariya da aka yi a tafiyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng