Wanda Ya Kafa NNPP ya Ƙaryata Bullar Baraka a Jam'iyya, ya Fadi Abin da ke Faruwa

Wanda Ya Kafa NNPP ya Ƙaryata Bullar Baraka a Jam'iyya, ya Fadi Abin da ke Faruwa

  • Yayin da ake samun musayar yawu daga wani sashe na jami'iyyar NNPP ga Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda ya kafa ta, Boniface Aniebonam, ya magantu
  • Dakta Boniface Aniebonam,ya bayyana cewa duk da matsalolin da ake samu, babu baraka ko rabuwar kai ko samar da bangaranci tsakanin 'yan jam'iyyar
  • Dakta Aniebonam ya kara da cewa akwai matsalar cikin gida, da ya hada da yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya dauki hukuncin sauya tambarin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Wanda ya kafa NNPP, Dakta Boniface Aniebonam, ya musanta cewa an samu baraka a cikin jam'iyyar, sai dai ya ce akwai matsala.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ci karo da matsala bayan sauya tambarin NNPP, mai jam'iyya ya yi masa gargadi

Ya ce duk da matsalar da ta kunno kai a cikin NNPP na zargin jagoranta na kasa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da daukar hukunci kai tsaye, babu bangare a cikinta.

Kwankwaso
Wanda ya kafa jam'iyyar NNPP ya ce babu baraka a jam'iyyar Hoto: Boniface Aniemobanam
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa matsala ce irin ta cikin gida NNPP ke fuskanta a halin yanzu, amma ba ta kai ga rarrabuwar jam'iyyar zuwa bangarori ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin NNPP: Aniebonam ya tabo Kwankwaso

Mai jam'iyyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam, ya ce wasu sun ga laifi a cikin yadda ya mika jagorancin jam'iyyar ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ya ce haka ne ma ya ba Kwankwaso damar sauya launin jam'iyyar ba bisa ka'ida ba, ba kuma tare da bin matakan da su ka dace ba, Independent News ta wallafa.

Wanda ya kafa NNPP ya ga laifin INEC

Dakta Aniebonam ya ce ba Sanata Kwankwaso ne kawai ke da laifi wajen sauya tambarin jam'iyyar NNPP ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sa labule da minista da manyan ƙusoshin APC a Abuja, an gano dalilin zaman

Ya ce kamata ya yi hukumar INEC ta tabbatar da sahihancin takardar shaidar jam'iyyar kafin ta amince da bukatar jagoran jam'iyyar.

Animeobonam ya caccaki Kwankwaso

A baya mun kawo labarin yadda wanda ya kafa jam'iyyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam, ya caccaki Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso saboda sauya tambarin jam'iyyar.

Boniface Aniebonam ya zargi dan takarar shugaban kasa karkashin NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da wargaza tsarin jam'iyyar daga gwadaben da aka kafa ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.