Tsige Ndume: Tinubu Ya Kara Rasa Goyon Bayan Manyan Yan Siyasa

Tsige Ndume: Tinubu Ya Kara Rasa Goyon Bayan Manyan Yan Siyasa

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya ba Bola Tinubu shawara kan korar Ali Ndume
  • Dele Momodu ya fadi haka ne a cikin wata wasika inda ya bayyanawa Bola Tinubu hakikanin halin da ake ciki a Najeriya
  • Har ila yau, Dele Momodu ya bayyana wadanda ya kamata Bola Tinubu ya ladabtar a cikin ministocinsa domin yin gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigon siyasa a kudancin Najeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu ya yi martani kan tsige Ali Ndume.

Dele Momodu ya bayyanawa Bola Ahmed Tinubu halin da Najeriya take ciki da matakin da ya kamata ya ɗauka.

Kara karanta wannan

Ndume: Maganar Sheikh Daurawa kan matsawa talaka a mulkin Tinubu ta tada ƙura

Dele Momodu
Jigo a siyasar kudu ya goyi bayan Ali Ndume. Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Dele Momodu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Momodu: 'Ana wahala a Najeriya'

Dele Momodu ya aika sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa lallai talakawa na shan wahala a Najeriya kamar yadda Ali Ndume ya fada.

Dan siyasar ya tabbatarwa Bola Tinubu cewa ko ba zai yarda da abin da ya fada ba dole zai fada masa gaskiya komai dacinta.

Momodu ga Tinubu: 'Ndume ya yi gaskiya'

Haka zalika Dele Momodu ya bayyanawa shugaban kasa Bola Tinubu cewa a halin yanzu yana bukatar mutane da za su rika fada masa gaskiya kamar Sanata Ali Ndume.

A kan haka ya bukaci Bola Tinubu ya yi taka tsantsan da yan siyasar da ke kewaye da shi kan cewa za su kai shi su baro shi.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kokari, kar ku shiga zanga zanga," Minista ya lallabi jama'a

Momodu: 'Ya kamata ka hukunta Wike'

Har ila yau Dele Momodu ya bayyana cewa ya kamata Bola Tinubu ya dauki mataki kan ministan Abuja, Nyesom Wike.

A cewar Dele Momodu, Nyesom Wike ya kwancewa Bola Tinubu zani a kasuwa kan yadda ya ki yarda da maganarsa a kan rikicin jihar Ribas.

Tinubu ya tura sako majalisar dattawa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa ya mika bukatarsa ga majalisa domin amincewa da karin tiriliyoyin Naira a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

A wasikar da shugaba Bola Tinubu ya aika ga majalisar, ya nemi a sahale masa karin Naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin na bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng