Yadda Aka Zane Masoyin Buhari, Dan Bilki Kwamanda Saboda 'Zagin' Gwamnan Kaduna
- Shafukan sada zumunta musamman Facebook sun dauki dumi bayan an wallafa bidiyon yadda wasu ke dukan masoyin Buhari a Kaduna
- A cikin bidiyon, an gano wasu mutane su na tuhumar AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda da zagin gwamna Uba Sani na jihar
- Duk da kiraye-kirayen da Dan Bilki ya rika yi na cewa ba shi da lafiya bai sa wanda ke dukansa ya tsagaita da shauda masa bulala ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu da ake zargin jami'an tsaro ne ke dukan daya daga masoyan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A bidiyon wanda a yanzu haka ya jawo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta, an gano wani mai farar riga ya na ta tsula wa AbdulMajeed DanBilki Kwamanda bulala.
An jiyo Dan Bilki Kwamanda na rokon wanda ke dukan shi inda ya ce ba shi da lafiya, kamar yadda aka gani a bidiyon da Muhammad Adam Tudun Murtala ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi Dan Bilki da zagin Gwamna
Wasu da ba a da tabbacin ko su waye sun rika dukan jigo a jam'iyyar APC na reshen jihar Kano, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda, kamar yadda Damagaran Post ta wallafa.
An jiyo mutanen na tambayarsa dalilin da ya sa ya ke zagin gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, yayin da shi kuma ke musanta haka.
Lokaci guda sai mai tambayar dalilin zagin gwamnan Kaduna ya ce a ba shi bulala, inda ya rika tsala masa, ya na cewa:
"Gwamna wasa ne? ka zama gwamna mana? Durkusa!"
Jami'an DSS sun cafke Dan Bilki
A baya mun ruwaito cewa jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun damke masoyin Buhari a Kano, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda bisa zargin cin zarafi.
Ana zargin Dan Bilki Kwamanda wanda ya shahara wajen shiga kafafen yada labarai da sukar 'yan adawa da cin zarafin tsohon gwamna kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa.
Asali: Legit.ng