An Ba Ndume Wani Muƙami Bayan Tsige Shi da Majalisa Ta Yi Daga Matsayi
- A jiya Talata ne majalisar dattawan Najeriya ta tsige Sanata Ali Ndume bisa umurnin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Biyo bayan tsige Sanata Ali Ndume, shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya nada shi sabon muƙami
- Har ila yau Sanata Godswill Akpabio ya yi kokarin ba da kariya ga Sanata Ali Ndume bayan an bukaci a hukunta shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Biyo bayan tsige sanata Ali Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa a majalisar dattawa ya samu sabon muƙami.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da mukamin da majalisa ta ba Ali Ndume.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa majalisar ta yi yunkurin hukunta Ali Ndume bayan tsige shi a jiya Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin tsige Ali Ndume a majalisa
Legit ta ruwaito cewa majlisar dattawan Najeriya ta tsige Ali Ndume daga matsayinsa ne bisa kalaman da ya yi a kan shugaban kasa.
Jam'iyyar APC mai mulki ce ta bukaci majalisar ta tsige Ali Ndume kuma ta nemi fita daga tafiyarta gaba ɗaya.
Sabon muƙamin Ali Ndume
Bayan tsige Ali Ndume, Sanata Godswill Akpabio ya nada Ali Ndume matsayin shugaban kwamitin harkokin bude ido, rahoton Punch.
A yanzu haka dai Sanata Ali Ndume zai cigaba da rike matsayin a majalisa yayin da ake jira ya yi martani kan fitarsa daga APC.
Yadda Akpabio ya ceci Ali Ndume
Bayan tsige Ali Ndume daga matsayinsa, Sanata Cyril Fasuyi ya bukaci a ladabtar da shi bisa laifin da ake ganin ya aikata.
Sai dai Sanata Akpabio ya nemi a yafe wa Ali Ndume kasancewar an riga an dakatar da shi daga mukaminsa.
Tinubu ya tura bukata ga majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa ya mika bukatarsa ga majalisa domin amincewa da karin tiriliyoyin Naira a cikin kasafin kudin shekarar 2024.
A wasikar da shugaba Bola Tinubu ya aika ga majalisar, ya nemi a sahale masa karin Naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kudin na bana.
Asali: Legit.ng