Fubara vs Wike: Gwamnonin PDP Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya a Rikicin Rivers
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna goyon bayansu ga gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara kan rikicin siyasar jihar
- Ƙungiyar gwamnonin a cikin wata sanarwa sun bayyana cewa akwai ɓuƙatar masu ruwa da tsaki su shawo kan matsalar
- Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike sun koma ba su ga maciji da juna saboda rikicin siyasar jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP sun bayyana goyon bayansu gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
Gwamnonin sun nuna goyon bayansu ga gwamnan ne kan rikicin siyasar jihar tsakaninsa da ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Ƙungiyar gwamnonin na PDP sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Fubara ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ƙarshen taronsu a Enugu, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin sun bayyana cewa ya kamata a tattauna sosai da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita kan rikicin siyasar da ke addabar jihar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Rikicin Fubara da Wike ya ƙi ƙarewa
Goyon bayan na su dai na zuwa ne yayin da ake fama da rikicin siyasa a jihar mai arziƙin man fetur.
Gwamna Fubara na cikin rikicin siyasa da magabacinsa Nyesom Wike, wanda yanzu yake kan kujerar ministan birnin tarayya Abuja.
Rikicin siyasar ya sanya majalisar dokokin jihar Rivers ta rabe gida biyu inda wani ɓangare na goyon bayan Wike yayin da wani ɓangaren ke goyon bayan Gwamna Fubara.
Matsayar gwamnonin PDP kan rikicin Rivers
"Ƙungiyar ta lura da rikice-rikicen da ke faruwa a reshen jam'iyyar PDP na jihar Rivers kuma a shirye take wajen tabbatar da zaman lafiya."
"Ƙungiyar ta yanke shawarar goyon bayan gwamnan jihar Rivers, mai girma Siminalayi Fubara."
- Ƙungiyar gwamnonin PDP
Gwamnonin sun bayyana cewa ya kamata a tattauna sosai da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita kan rikicin siyasar da ke addabar jihar.
Rikicin PDP ya ƙara ƙamari a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin jam’iyyar PDP a jihar Ribas ya kara kamari, biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke na hana shugabannin jam’iyyar gudanar da babban taronta.
Babbar kotun da ke zamanta a Port Harcourt, babban birnin jihar, ta hana jam’iyyar gudanar da taron da ta shirya yi a ranar 27 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng