Kwankwaso Ya Ci Karo da Matsala Bayan Sauya Tambarin NNPP, Mai Jam'iyya Ya Yi Masa Gargadi

Kwankwaso Ya Ci Karo da Matsala Bayan Sauya Tambarin NNPP, Mai Jam'iyya Ya Yi Masa Gargadi

  • Yayin da Rabi'u Kwankwaso ya sauya tambarin NNPP, ya gamu da cikas daga wanda ya kirkiro jam'iyyar adawar a Najeriya
  • Dakta Boniface Aniebonam ya caccaki Kwankwaso da hukumar INEC kan sauya tambarin da kuma launin jam'iyyar gaba daya
  • Aniebonam ya ce ya tsara jam'iyyar tun 2001 yadda za ta kawo sauyi a ƙasa amma zuwan Kwankwaso da wasu ya lalata komai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Uban jam'iyyar NNPP a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam ya caccaki Rabiu Kwankwaso kan sauya tambarin jam'iyyar.

Aniebonam ya yi fatali da matakin Kwankwaso wanda kuma ya yi gyaran fuska a kundin tsarin mulkin jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi kamu, babban jigon da ya yaƙi tikitin Musulmi da Musulmi ya koma APC

Uban jami'yyar NNPP ya caccaki Kwankwaso kan sauya tambarinta
Dakta Boniface Aniebonam ya soki matakin Rabiu Kwankwaso na sauya tambarin jam'iyyar NNPP. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

NNPP: Aniebonam ya dira kan Kwankwaso

Aniebonam ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a birnin Abuja, kamar yadda Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'assasin jam'iyyar ya koka kan yadda Kwankwaso ya shirya taron kasa na NNPP duk da umarnin kotu a kan haka, cewar Punch.

Ya kuma caccaki hukumar zabe ta INEC da amincewa da sauya tambari da launi da kuma gyaran fuska a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Aniebonam ya fadi yadda suka tsara NNPP

Har ila yau, Aniebonam ya ce tun 2001 da ya kafa jam'iyyar sun ba kowane dan kasa damar shiga amma zuwan Kwankwaso ya lalata komai.

Ya ce babu wanda ya isa ya kore shi a jam'iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin NNPP ya ce tun da satifiket dinta ya na hannunsa har yanzu.

"Kwankwaso da wasu marasa aikin yi da suke tare suna ta cewa wai sun kori wanda ya assasa jam'iyyar, ba ku tunanin suna da wata matsala tattare da su?".

Kara karanta wannan

Ganduje ya buƙaci Sanata ya fice daga APC mai mulki ya koma jam'iyyar adawa

- Dakta Boniface Aniebonam

Kwankwaso ya yi wa El-Rufai tayi zuwa NNPP

Kun ji cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi tayi na musamman ga Nasir El-Rufai domin shiga jam'iyyarsu ta NNPP.

Kwankwaso ya ce kofar jamiyyar a bude take ga kowane ɗan Najeriya inda ya ce bukaci tsohon gwamnan ya shigo idan yana so.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.