Gwamna Ya Jawo Mutane a Jiki, Ya Naɗa Sababbin Hadimai Sama da 1,000
- Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya fitar da jerin sunayen mutane 1,270 da ya naɗa a muƙamai daban-daban a gwamnatinsa
- Sakataren gwamnatin Taraba, Gebon Kataps ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa, ya ce gwamnan zai yi naɗe-naɗen ne a rukuni hudu
- Duk da har kawo yanzu ba a bai wa mutanen wuraren aiki ba amma gwamnatin ta ce za su yi aikin mashawarta na musamman da majalisar hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya naɗa sababbin hadimai 1,270 da za su taimaka masa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya naɗa jimullar hadimai 1,075 a cikin sa'o'i 24 tsakanin ranar Litinin 15 zuwa ranar Talata 16 ga watan Yuli 2024.
Sakataren gwamnatin jihar Taraba, Gebon Kataps ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muƙaman da Gwamna Kefas ya naɗa
Ya ce mutanen da gwamna Kefas ya naɗa sun haɗa da mashawarta na musamman, manya da ƙananan mataimaka na musamman.
Sauran sun haɗa da 'yan majalisar gudanarwa na hukumomin gwamnatin jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Gwamnan Taraba ya yi ruwan mukamai
A ranar Litinin da ta gabata gwamnatin jihar ta fitar da jimillar sunayen mutane 573 da gwamnan ya naɗa a mukamai, sannan ta fitar da mutane 502 a daren ranar Talata.
Gwamnatin ta kuma ƙara mutane 195 a jimullar sunayen da aka fitar, amma har kawo yanzu gwamnan bai rabawa mutane wuraren da za su yi aiki ba.
Waɗannan naɗe-naɗe sun biyo bayan wasu mutane biyar da gwamnan ya bai wa muƙamai a gwamnatinsa kwanan nan, cewar rahoton Vanguard.
A halin yanzu ana dakon kashin karshe na sunayen waɗanda Gwamna Kefas zai naɗa saboda tun farko gwamnatin Taraba ta ce za a yi naɗe-naɗen ne a rukuni huɗu.
Kwamishinoni 2 sun yi murabus a Abia
A wani labarin kuma Kwamishinoni biyu sun miƙa takaradar murabus daga mukamansu a majalisar zartaswa ta jihar Abia da ke Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun nuna cewa kwamishinonin da suka ɗauki wannan matakin sune na ma'aikatar kimiyya da fasaha da ma'aikatar noma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng