PDP Ta Dauki Mataki Bayan Nade Naden Gwamna Sun Bar Baya da Kura

PDP Ta Dauki Mataki Bayan Nade Naden Gwamna Sun Bar Baya da Kura

  • Jam'iyyar PDP a jijar Taraba da kwantar da hankulan mambobinta waɗanda naɗe-naɗen da Gwamna Agbu Kefas ya yi bai musu daɗi
  • Kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa ya kamata waɗanda ba su gamsu da naɗe-naɗen ba da su yi haƙuri saboda Allah ke ba da mulki
  • Ya bayyana cewa ba zai yiwa gwamnan ya raba muƙamai ga ƴaƴan jam'iyyar ba a lokaci ɗaya saboda yawan da suke da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Jam’iyyar PDP a jihar Taraba ta buƙaci magoya bayanta da su yi taka tsan-tsan tare da kaucewa tayar da ƙura kan naɗe-naɗen da Gwamna Agbu Kefas ya yi a baya-bayan nan.

Jam’iyyar ta yi wannan roƙo ne biyo bayan yadda ake ta sukar tsofaffin ƴan siyasa da Gwamna Kefas ya naɗa muƙamai.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ƙara rusa ƴan adawa, manyan jiga-jigai da dubban mutane 4450 sun koma APC

PDP ta kwantar da hankulan mambobinta a Tara
Nade-naden Gwamna Kefas sun bar baya da kura a Taraba Hoto: @AgbuKefas
Asali: Twitter

Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar, Hassan Kona ya nuna rashin jin daɗinsa kan nade-naden da gwamnan ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da manema labarai a Jalingo, mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Andetarang Irammae, ya yi kira da a kwantar da hankula, cewar rahoton jaridar Tribune.

Me PDP ta ce kan naɗe-naɗen Gwamna Kefas?

Ya kuma ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin cewa jam’iyyar da gwamnatin Kefas sun damu da damuwarsu, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.

Jam’iyyar ta kawar da fargabar da ake ta samu a wasu ɓangarori na yadda aka yi watsi da waɗanda suka wahalta mata ta samu nasara a zaɓen shekarar 2023.

Ya bayyana cewa duk da Hassan Kona yana da ƴancin faɗar ra'ayinsa kan naɗe-naɗen da gwamnan ya yi a matsayinsa na ɗan jam'iyya, bai kamata ya tayar da hayaniya ba saboda Allah ne ke ba da mulki.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya dau zafi yayin da aka kori tsohon dan majalisa ana dab da zaben gwamna

"Tabbas ya yi tunanin cewa za a sanya sunansa a cikin jerin, amma lokacin da ya gano babu sunansa, a wajensa wannan ita ce hanyar da zai nuna ɓacin ransa."
"Amma ya kamata ya sani cewa jam'iyyar tana da mambobi kusan miliyan ɗaya kuma ba zai yiwu a ba kowa muƙami ba a lokaci ɗaya."
"Sai dai a riƙa bayarwa a hankali a hankali, ina roƙo ga mutane irinsa da su kwantar da hankulansu sannan su ci gaba da marawa gwamnati baya."

- Andetarang Irammae

Gwamna Kefas na adawa da ƴan sandan jihohi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya nuna adawa da shirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohi da ake yi a ƙasar nan.

Gwamnan ya dage cewa hukumomin tsaron da ake da su a ƙasar nan na da ƙarfin magance ƙalubalen tsaro da ke addabar al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng