Muhimman Abubuwa 6 Game da Sanatan da Ya Karɓi Matsayin Ndume a Majalisa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024 jam'iyyar APC ta naɗa Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa a matsayin mai tsawstarwa a majalisar dattawa.
Sanata Tahir Mungono ya maye gurbin Muhammed Ali Ndume wanda aka sauke daga muƙamin sakamakon sukar da ya yiwa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Tahir Mungono ya canji Ali Ndume
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da sauyin da APC ta yi a zaman majalisa na ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasikar da APC ta aika majalisar mai ɗauke da sa hannun Ganduje, ta buƙaci Ali Ndume ya koma duk jam'iyyar adawar da ta kwanta masa a rai.
Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon mai tsawatarwa, Tahir Mungono, ga su kamar haka:
1. Haihuwar
An haifi Muhammed Tahir Mungono a ranar 12 ga watan Fabrairu, 1966 a garin Mungono da ke jihar Arewa a wancan lokaci wanda yanzu ya koma ƙarƙashin jihar Borno.
2. Ilimi
Tahir Mungono ya yi karatun firamare a Monguno Central Primary School daga nan ya wuce makarantar sakandiren gwamnati (GSS) da ke garin Ngala a jihar Borno.
Bayan ya karbi shaidar kammala sakandire (SSCE) Tahir ya karanci fannin sanin shari'a watau Lauya a jami'ar jihar Borno, inda ya gama a shekarar 1989.
Ya halarci Makarantar lauyoyi ta Najeriya kuma ya zama cikakken lauya a shekarar 1990.
3. Ya riƙe mukaman kwamishina a Borno
Ya rike mukamin kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na jihar Borno daga 2003 zuwa 2005.
Tahir Mungono ya rike kwamishinan ilimi duk da bai jima ba a tsakanin 2005 zuwa 2006, sannan aka mayar da shi ma'aikatar albarkatun ruwa a 2006 zuwa 2007 duk a jihar Borno.
4. Yadda ya shiga majalisar tarayya
A shekarar 1992, Tahir Monguno ya tsaya takara kuma al'umma suka zabe shi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar Marte, Monguno sa Nganzai yana da shekaru 26.
Ya samu wannan nasara ne gabanin juyin mulkin sojoji na 1993 wanda ya kai ga kawo karshen wa'adin dukkan zababbun wakilai.
An sake zaben shi a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar Marte/Nganzai/Monguno daga jihar Borno a shekarar 2007.
Tahir Mungono ya yi aiki a matsayin ɗan majalisa a majalisar wakilan tarayya ta 7, 8 da kuma majalisa ta 9.
5. Ya nemi kujerar shugaban majalisar wakilai
A majalisa ta 9 da aka kafa a 2019, Tahir Monguno yana daya daga cikin na sahun gaba a masu neman kujerar kakakin majalisar wakilan Najeriya a jam'iyyar APC.
Sai dai daga baya ya janye daga takarar tare da goyon bayan Femi Gbajabiamila wanda shi ne zabin jam'iyyar mai mulki.
Bayan haka ne aka naɗa Tahir Mungono a matsayin mai tsawatarwa a majalisar wakilai daga ranar 4 ga watan Yuli, 2019 zuwa 11 ga watan Yuli, 2023.
6. Sanatan Borno ta Arewa
A zaɓen 2023, Muhammed Tahir Mungono ya samu nasarar lashe zaɓen sanata mai wakiltar Borno ta Arewa a majalisar dattawa ta 10.
A halin yanzu kuma jam'iyyar APC ta naɗa shi a matsayin mai tsawatarwa bayan sauke takwaransa na Borno ta Kudu, Ali Ndume.
APC ta nemi Ndume ya bar jam'iyya
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta shawarci sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammed Ali Ndume ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar adawa
Hakan ya biyo bayan sauke Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalisar dattawa sakamakon sukar da ya yiwa Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng