Gwamna Ya Gamu da Cikas, Kwamishinoni 2 Sun Yi Murabus Daga Muƙamansu
- Kwamishinoni biyu sun miƙa takaradar murabus daga mukamansu a majalisar zartaswa ta jihar Abia da ke Kudu maso Gabas
- Rahotanni sun nuna cewa kwamishinonin da suka ɗauki wannan matakin sune na ma'aikatar kimiyya da fasaha da ma'aikatar noma
- Yayin da aka fara jita-jitar Gwamna Alex Otti ne ya kore su, mai magana da yawun gwamnan ya ce babu wanda aka kora
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Rahotanni daga jihar Abia a Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna cewa wasu kwamishinoni biyu sun yi murabus daga kan muƙamansu.
Kwamishinonin sun yi murabus daga kujerunsu a majalisar zartaswan jihar Abia karkashin jagorancin Gwamna Alex Otti a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, waɗanda suka yi murabus din sun haɗa da kwamishinan kimiyya da fasaha, Chima Oriaku da kwamishinar noma, Farfesa Monica Ironkwe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kwamishinonin suka yi murabus?
An tattaro cewa labarin murabus din kwamishinonin ya fara yaɗuwa ne jim kaɗan bayan taron majalisar zartaswa ta jihar wanda Gwamna Otti ya jagoranta.
A rahoton Vanguard, wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa mai girma gwamna ne ya kori kwamishinonin, wasu kuma sun ce bisa radin kansu suka yi murabus.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnan ko kwamishinan yada labarai, Prince Okey Kanu game da lamarin.
Lamarin ya biyo bayan dakatar da kwamishinar lafiya Dr. Ngozi Okoronkwo a kwanakin baya a wani taron majalisar zartarwa ta jiha wanda gwamnan ya jagoranta.
Gwamna Otti ya kori kwamishinoni 2?
Da yake mayar da martani kan labarin da ke yawo, babban sakataren yada labaran gwamnan Abia, Ukoha Njoku Ukoha, ya yi karin haske da cewa babu wanda aka kora.
"Kwamishinonin biyu sun yi murabus ne da kansu, ba a a kori kowa ba. Ku yi watsi da jita-jitar da mutane ke yaɗawa,"
- Ukoha Njoku Ukoha
Abia ta ƙarawa ma'aikata N45,000
A wani rahoton kun ji cewa Gwamnatin jihar Abia ta amince da biyan ma'aikatan jihar N15,000 tsawon watanni uku wanda zai kama N45,000 domin rage musu radadi.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai a jihar, Prince Okey Kanu ya fitar a jiya Litinin 15 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng