Jerin Gwamnoni 13 da Suka Fara Gaggawar Shirya Zabe Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli
Akalla gwamnoni 13 ne suka farga suka fara shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a jihohinsu bayan hukuncin kotun ƙoli a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Idan ba ku manta ba, kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta yanke cewa haramun ne gwamnoni su riƙa danne kuɗaɗen kananan hukumomi da aka turo daga tarayya
Kotu ta ba kananan hukumomi 'yanci
Ta kuma bayyana cewa daga yanzu ƙanannan hukumomi 774 na da haƙƙi da ikon tafiyar da kason kuɗinsu, inda ta umarci a tura masu kudi kai tsaye.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a ƙarar da Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'a ya shigar da gwamnonin jihohi 36.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau kotun ta bayyana cewa kantomomi da gwamnoni ke naɗawa sun saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, Punch ta ruwaito.
Legit.ng ta tattaro muku gwamnonin da suka sanya ranar zaɓen kananan hukumomi bayan wannan hukunci, ga su kamar haka:
1. Uba Sani na Kaduna
Hukumar zaɓen Kaduna (KAD-SIECOM) ta sanar da cewa ranar 19 ga watan Oktoba, 2024 za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi a faɗin jihar.
Shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a Kaduna sun shiga ofis ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2021 kuma wa'adinsu zai ƙare ranar 31 ga watan Oktoba, 2024, rahoton Channels tv.
2. Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi
Kamar dai Kaduna, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kogi ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.
Shugaban hukumar, Mamman Eri ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana ranar Talata a birnin Lokoja.
Mamman ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulki wanda ya ɗora alhakin shirya zaɓen a wuyan hukumar.
3. Bala Mohammed na Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ba a bar shi a baya ba yayin da hukumar zaɓen jihar ta zaɓi ranar 19 ga watan Agusta domin gudanar zaɓen ciyamomi da kansiloli.
Shugaban hukumar zaɓen Bauchi mai zaman kanta, Alhaji Ahmed Makama ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Talata.
Ahmed Makama ya tabbatar da cewa sun yi dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.
4. Malam Dikko Radda na Katsina
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar Asabar 15 ga Fabrairu, 2025.
Shugaban KTSIEC, Alhaji Lawal Alhassan Faskari, ya karfafa wa masu sha’awar tsayawa takara daga jam’iyyun siyasar da aka amince da su guiwarsu fito a fafata da su.
5. Gwamna Adeleke na jihar Osun
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun (OSIEC) ta bayyana cewa ba zata yi gaggawar gudanar da zaben kananan hukumomi ba duk da hukuncin kotun koli.
A cewar shugaban OSIEC Hashim Abioye, hukumar tana nan a kan jadawalin zaben da ta fitar a baya wanda ta tsara yin zaɓen a watan Fabrairu, 2025, cewar The Nation.
Sauran gwamnonin sun haɗa da:
S/N | Jiha | Sunan gwamna | Ranar zaɓe |
6 | Enugu | Peter Mbah | 5 ga watan Oktoba, 2024 |
7 | Benuwai | Hyacinth Alia | 16 ga watan Nuwamba, 2024 |
8 | Ribas | Siminalayi Fubara | 5 ga watan Oktoba, 2024 |
9 | Jigawa | Umar Namadi | 14 ga watan Yuni, 2024 |
10 | Imo | Hope Uzodinma | Watan Satumba, 2024 |
11 | Kebbi | Dr. Nasir Idris | 31 ga watan Augusta, 2024 |
12 | Abia | Alex Otti | Babu takamaiman kwanan wata |
13 | Anambra | Charles Soludo | Babu takamaiman kwanan wata |
Gwamnan Eno ya yi maraba da hukuncin kotu
A wani rahoton kuma Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ce bai taɓa ɗaukar ko sisi daga kason kuɗin da ake turo ma kananan hukumomin jihar ba.
Fasto Umo Eno ya yi maraba da hukuncin kotun koli na bai wa kananan hukumomi cikakken ƴancin karbar kason kudinsu daga tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng